Jirgin Ethiopian airlines na kasar Habasha ya yi hatsari
March 10, 2019'Yan kasar kenya na kan gaba a jerin 'yan kasashen wajen da suka hallaka sakamakon hatsarin jirgin saman kamfanin Habasha na Ethiopian airlines. Kasashen 32 ne lamarin ya shafa da suka hada da 'yan Kanada (18) 'yan Habasha (9) 'yan Italiya (8) China (8) Amirka (8) Birtaniya (7) Faransa (7) Nerland (5) Indiya (4) sai ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya 4.
Kamfanin Ethiopian airlines mallakar kasar ta Habasha ya ce tuni ya aike da tawagar ma'aikatansa da za su taimakawa masu bayar da agaji a yankin Bishoftu na Oromo da ke kudancin kasar wurin da jirgin ya yi hadarin, to amma sai dai kamfanin ya ce ba wanda ya tsira da ransa kawo yanzu daga faduwar jirgin.
Tuni dai Firaministan kasar Abiy Ahmed, da Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta suka wallafa sakon juyayi da kuma jaje ga iyalan wadanda aka rasa a hatsarin. Ita ma dai kungiyar Tarayyar Afirka ta bakin shugabanta Moussa Faki Mahammat ya aikewa iyyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su sakon ta'aziya.