1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

March 1, 2005

Ibrahim Jaafari mutumin dake kan gaba a neman faraminista a iraqi.

https://p.dw.com/p/Bvcx
Hoto: AP

Ya zuwa yanzu dai babban abinda yafi daukar hankalin yan kasar ta iraqi shine ci gaba da nuna alhini ga iyalan wadan da harin bom din nan na jiya litinin ya rutsa dasu a yankin hilla dake birnin Bagadaza.

Idan dai za a iya tunawa dan kunar bakin waken ya tashi bom din ne a cikin gungun masu neman aiki dake tsai tsaye suna jiran a gudanar da bincike na kwakwaf a jikin su kafin a tabbatar musu da wan nan aikin na gwamnati.

Jim kadan dai da tashin wan nan bom mutane a kalla 125 suka rasa rayukan su a hannu daya kuma da yawa suka jikkata.

Wan nan dai tashin bon a yanzu haka na a matsayin irin sa mafi muni daya fi na kowane lokaci muni a tun lokacin da sojojin taron dangi karkashin jagorancin amurka suka kawar da gwamnatin tsohon shugaba Saddam Hussain.

Rahotanni da suka iso mana daga iraqi a yanzu haka na nuni da cewa a yanzu haka jamian yan sanda na kasar sun kaddamar da bincike na dalilin kai wan nan hari a cikin gungun masu neman aikin gwamnatin, to amma ya zuwa yanzu babu wani ko wata da aka kama da zargin hannu a cikin tashin bom din.

Ya zuwa yanzu dai da yawa daga cikin shugabannin kasashen duniya sunyi tofin allah Tsine game da wan nan balai daya afkawa kasar ta iraqi.

Bisa hakan sun bukaci da a gaggauta daukar kwararan matakai na dakile faruwar irin haka a nan gaba don ganin an samar da tabbataccen zaman lafiya a fadin kasar ta iraqi baki daya.

A dai dai lokacin da kasar ta iraqi ke fuskantar wadan nan rikice rikice da tashen tashen bama bamai kuwa a dai dai lokacin ne manya manyan yan siyasar kasar keci gaba da tunanin zaben mutanen da suka cancanta wajen jan ragamar sabuwar gwamnatin da za a kafa bayan gudanar da zaben gama gari.

A waje daya kuma wani gidan talabijin ya nuna hoton yar jaridar nan ta kasar faransa da akayi garkuwa da ita tana neman da ayiwa Allah ayiwa annabi a ceci ranta daga hannun wadan da suka yi garkuwa da itan.

Har ilya yau yar jaridar mai suna Florence Aubenas taci gaba da yin bayanin cewa tana cikin mawuyacin hali na kakanikayi sakamakon rashin tsabtza na gurin da take zaune.

A dai tun lokacin da aka cafke ta tare da wani mai mata fassara kusan watanni biyu da suka gabata babu duriyar su sai a wan nan lokaci.

A yanzu haka dai a cewar wani dan majalisa na kasar faransa mai suna Julia, yana nan yana kokarin gabatar da batun yar jaridar don sanin matakin daya kamata a dauka na kubutar da Florence daga cikin halin data fada.

Bugu da kari bayanai sun kuma tabbatar da cewa har yanzu an rasa jin duriyar inda yar jaridar nan ta kasar italiya take wato Giuliana Sgrena wacce akayi garkuwa da ita a watan fabarairun daya gabata na wan nan shekara.

Ibrahim sani.