1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki bayan harin bam a Kano

March 19, 2013

Rundunar 'yan sandan kano ta tabbatar da cewar wata mota kirar Golf shudiya ce ta kai harin kunar bakin wake kuma tuni rundunar ta bazama domin farautar masu kai harin.

https://p.dw.com/p/180IQ
A security man walks pass the charred remains of buses after Monday's explosions at a bus park in Sabon Gari in Kano March 19, 2013. Five explosions at the bus park in northern Nigeria's main city of Kano killed at least 25 people on Monday, a Reuters witness said, in an area where Islamist sect Boko Haram is waging an insurgency against the government. The coordinated bombing came as an audio tape emerged of a man saying he was the father of a family of seven French tourists kidnapped by Boko Haram militants. REUTERS/Stringer (NIGERIA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS)
Hoto: Reuters

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana cewar mutane 22 ne aka tabbatar da mutuwarsu a sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai tashar manyan motocin safa dake sabon garin kano dake arewacin Najeriya, sai dai kuma shugabannin kabilar Igbo mazauna jihar na cewar da kansu sun kirga gawarwaki sama da 60, baya ga wasu da suka jikkata, haka kuma wayewar garin yau, wasu mutane dauke da bindigogi sun harbe wata 'yar sanda dake kan hanya zuwa wurin aiki.

Da safiyar yau ne rundunar 'yan sandan ta yi taron manema labarai in da ta bayyana cewar bayan kammala tattara bayanai da rundunar tayi yanzu haka mutane 22 aka tabbatar sun kwanta dama baya ga wasu da suka jikkata, sai dai ana ta bangaren kungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo, ta bayyana cewar da hannunsu sun kirga wadanda suka rasu sama da 60, shugaban kungiyar a jihar Kano chief Tobayas Michel Idika, ya tabbatar da cewar sun sami wannan alkaluma ne, yayin aikin ceto da aka aiwatar tun lokacin da farmakin ya faru, harma ya bayyana cewar wannan farmakin an yi shine ga kabilar Igbo da kuma kadarorinsu, sai dai kwamishinan 'yan Sandan jihar Kano musa Abdulsalam Daura ya ce alkalumansu shine daidai.

Ausgebrannter Bus nach einem Bombenanschlag auf die New Road Bus-Station in Kano/Nigeria. Der Anschlag wurde am Abend des 18.3.2013 verübt. Bild: DW, 19.3.2013, Kano/Nigeria
Hoto: DW

Dangane da kukan da kabilar ta Igbo ke yi a cewar su aka kaiwa wannan hari mutane da dama a ganin cewar, hari ne da ya shafi dukkan kabilu kamar yadda wani mutum Abdellateef Oalabode ya bayyana.

Har ila yau da safiyar talatar nan ce wasu mutane dauke da bindigogi suka biyo bayan wata jami'ar 'yan sanda dake aiki da shiyya ta daya ta rundunar 'yan sanda dake kano, in da suka bude mata wuta a unguwar farm center, nan take kuma ta rasa ranta kamar yadda kwamishinan 'yan sandan ya tabbatar.

Ire iren wadannan hare hare dai na ci gaba da firgita mutane musamman wadanda suke baki a jihar lamarin da yasa suke tunanin fitar da iyalansu daga Kano, kamar yadda wani kabilar Igbo daya nemi a sakaya sunansa ya bayyana.

Rundunar 'yan sandan Kano ta tabbatar da cewar wata mota kirar Golf shudiya ce ta kai wannan harin kunar bakin wake kuma tuni rundunar ta bazama domin farautar masu hannu a cikin harin.

Mawallafi : Nasir Salisu Zango
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Nuna karin labarai