1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da Iraki ke ciki bayan kawar da Saddam

April 9, 2013

Shekaru goman da suke wuce ne Amurka ta hambarar da Saddam Hussein daga karagar mulkin kasar Iraki. Sai dai har yanzu kasar na fama da rikici na siyasa da kuma na addini, wadanda ba san karshensu ba.

https://p.dw.com/p/18CRO
FILE - A U.S. Marine watches a statue of Saddam Hussein being toppled in Firdaus Square in downtown Baghdad on April 9, 2003 file photo. (AP Photo/Jerome Delay, File)
DW 60 Jahre Irak Saddam Hussein Statue 09.04.2003Hoto: picture alliance/AP Photo

kasar Amurka ta nunar da cewa akwai ci gaba mai ma'ana da aka samu a Iraki bayan hambarar da Saddam Hussein daga karagar mulki shekaru goman da suka gabata. A lokacin wata ziyarar aiki da ya kai birnin Bagdaza Sakataren Harkokin Wajen wannan kasa John Kerry ya ce ko ba komai, dimbin 'yan Iraki sun samu 'yancin fadan albarkacin baki da kuma 'yancin gudanar da gangami na siyasa. Sai dai kuma ya amince cewa har yanzu da jan aiki a gaban hukumomi wajen mayar da ita kan turba ta zaman lafiya.

Anschlag auf schiitische Gläubige im Irak
'yan sunnin da 'yan shi'an Iraki na kai wa jinansu hare hare.Hoto: Reuters

Har ya zuwa yanzu dai harkokin mulki na tafiyar hawainiya, yayin da tashe-tashen hankula da kuma cin zarafin jama'a ke neman zama ruwan dare a Iraki. Hasali ma dai kungiyoyin 'yan tarzoma da ke da alaka da al-Qa'ida na cin karensu ba tare da babbaka ba. Saboda haka ne ma kungiyoyi da suka himmantu wajen kare hakkokin jama'a a Iraki suke sukar Amurka game da rawar da ta taka wajen cin zarafin fursunonin siyasa. Erin Evers, jami'a a kungiyar Human Right Watch ta ce tabargazar da Amurka ta tafka a gidan yarin Abou Ghraib ya shafa mata kashin kaji ainin.

"Kafin shekarun 2002 da 2003 ana kallonmu da kima a duniya baki daya a fannin kare hakkin bani Adama. Amma dai daga bisani ta zube. karkashin mulkin Obama ma, ba mu samu mun farfado da ita ba. A shekara ta 2009, bai hukunta manyan jami'ai da suka yi tabargazar gidan yarin Abou Ghraib ba. Wannan kuwa babban kuskure ne."

Abu Ghraib
Amurkawa sun yi ba daidai ba a gidan yari Abu GhraibHoto: AP

Matakin wanke kanta da Amurka ta dauka

A halin yanzu dai  amurkawa 10.500 ne ke ci gaba da aiki a kasar ta Iraki ciki kuwa har da jami'an diplomasiyya da jami'an tsaro da sauransu. Sai dai fadar mulki ta Washington za ta rage rabin ma'aikatanta kafin karshen wannan shekara ta 2013. Da ma kuma ta janye akasarin sojojinta tun a karshen shekara ta 2011. Ita dai gwamnatin Iraki ta nunan alamun yafewa sojojin Amurka da suka ci zarafin fursunoni a gidan yarin Abou Ghraib laifinsu. Amma kuma Amurka ta ce akai kasuwa a cewar Peter Feaver, malamin kimiyar siyasa a jami'ar Duke.

10 Jahre Irakkrieg
Har yanzu ba wani haske a al'amuran mulkin Iraki.Hoto: AFP/Getty Images

"Firaminista al-Maliki a shirye ya ke ya yafe wa sojojin Amurka tabargazar da suka tafka. Amma kuma babban mai shigar da kara na Amurka ya bukaci Majalisar Dokoki ta albarkanci wannan doka."

Mahawara game da kawar da Saddan Hussein

Al'amuran tsaro na dada tabarbarewa a kasar ta Iraki musamman ma a larduna 18 da za a gudanar da zabe a ranar 20 ga wannan wata na Afirilu. Wasu daga cikin al'umar wannan kasa na cewa gara jiya da yau a fannoni daban-daban na rayuwa. Dalilin da suka bayar shi ne mulkin danniya ne kawai suka yi fama da shi karkashin shugabancin saddam Hussein. Amma ba a fuskantar matsaloli na tsaro da kuma karancin kayan bukatun yau da kullum. Sai dai Jim Philips jami'i a gidauniyar Heritage Foundation ya ce  kawar da Saddam Hussein wani alhairi ne ga Iraki baki daya.

"Da a ce Amurka ba ta afkawa Iraki shekaru goman da suka gabata tare da kawar da Saddam Hussein daga kujerar mulki ba, da akwai yiwuwar ya ci gaba da kashe talakawa, sannan mai yiwuwa ya kaddamar da wani yaki."

US-Außenminister John Kerry mit irakischem Premierminister al Maliki
Sakataren tsaron Amurka Kerry da firaministan Iraki al-Maliki na gudanar da shawarwariHoto: Reuters

Ra'ayoyin amurkawa na ci gaba da banbanta game da kawar da Saddan Hussein daga kujerar mulki da kasarsu ta yi. Kiddidigar jin ra'ayin jama'a da cibiyar Pew ta gudanar ta nunar da cewa kashi 44% na ganin cewa yakin Iraki wani babban kuskure ne, yayin da kashi 41% na amurkawa suke na'am da kawar Saddam Hussein da aka yi.

Rahotanni ciki sauti na kasa

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou