1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas da Isra'ila na aiki da tsagaita wuta

August 14, 2014

Isra'ila da Falasdinawa na neman hanyoyin tsagaita wuta mai dorewa.

https://p.dw.com/p/1Cuki
Hoto: picture-alliance/AP

Bangarorin Isra'ila da Falasdinawa sun bai wa kansu wa'adin kwanaki biyar na gabatar da daftarin tsagaita wuta a yankin Zirin Gaza. Masu shiga tsakani sun yi maraba da amincewa da tsawaita tsagaita wuta da bangarorin suka yi, amma akwai sauran aiki.

Bisa sabon shirin sulhu da kasar Masar ta gabatar za a ci gaba da tsagaita wuta zuwa ranar 18 ga wannan wata na Agusta, kuma an amince da karin wadannan kwanakin biyar jim kadan kafin wa'adin kwanaki uku da ake amfani da shi ya cika. Bangarorin na Falasdinawa da Yahudawa da ke tattaunawa sun bar birnin Alkahira na kasar Masar, domin komawa gida su tattauna lamari na gaba da shugabanninsu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Ediat: Mohammad Nasiru Awal