1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi ya kirkiro na'urar majigi ta koyarwa

October 24, 2018

Wani matashi a jihar kano ya kirkiro na'urar majigi don saukaka hanyoyin koyarwa a makarantu.

https://p.dw.com/p/377qS
Nigeria Makoko schwimmende Schule in Lagos
Wani malami a Lagos yayin da yake koyarwa a aji.Hoto: Reuters/A. Akinleye

Wani matashi a jihar kano ya kirkiro na'urar nuna majigi don saukaka hanyoyin koyarwa ta yadda ilimin dalibai zai kara inganta.

A cewar matashin, ilimi ya kan inganta ne a cikin sauki matukar dalibai za su ji, su kuma ga abubuwan da ke kunshe a cikin darussan da ake koya musu.

Matashin Anas Balarabe Yazid ya kirkiri na’urar ta majigi da ya sa mata suna Yoda har iri uku kuma sun banbanta da nau’rorin majigi da aka saba hada su da kwamfuta kafin su yi aiki.

Matashin yace ya yi tunanin kirkiro da naurar ta majigi bayan da ya lura da banbancin tsarin karatun Najeriya mai wahalar fahimta da kuma Ingila inda ya yi karatun digirinsa na biyu wanda yake mai saukin fahimta, saboda yaro zai ji ya kuma ga irin majigin darasin da ake koya masa.