1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutunta wa’adin mulki a kasashen Afirka

Salissou Boukari AMA
October 4, 2019

Tsoffin Shugabannin Afirka sun kammala taro kan batun mutunta wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanadar a kasashen Afirka a wani mataki na samar da dimukuradiyya mai armashi da shimfida zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/3Qkni
Niger Niamey Ex-Präsidenten Gipfel
Hoto: DW/Salissou Boukari

An samu halartar tsaffin shugabannin kasashen Afirka da su hada da Goodluck Jonathan na Najeriya da Nicéphore Soglo na kasar Benin da Amos Sawyer na Liberiya da Catherine Samba-Panza da kuma Mahamane Ousmane na Jamhuriyar Nijar da suka halarci kaddamar da taron, a yayin da  tsofuwar shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf da tsofon shugaban kasar Saotome Michel Travadota suka yi magana kai tsaye da zauren taron ta faifan bidiyo.
Tsawon kwanaki uku tsaffin shugabannin da sauran kwararru suka shafe suna nazari nazari kan hanyoyin bi domin ganin kasashen Afirka sun yi biyayya ga wa’adin mulkin dimukuradiyya, da hanyoyin da dokokin kasshensu suka tanada. Cibiyar National Institut for democratie (NDI) ce ta shirya wannan zaman taro da hadin gwiwar manyan kungiyoyi irin su OSIWA da Forum Afrika ta tsaffin shugabannin kasashe Afirka matakin da mataimakin kungiya ta tsaffin shugabannin Afirka kuma tsofon shugaban kasar Benin Nicephore Soglo ya bayyana da matukar muhimmanci inda ya ce taro ya samar da hanyoyin bunkasa tsarin dimukuradiyya da mika mulki cikin ruwan sanyi kaman yadda dokokin kasashe suka tanada, inda ya yaba da musanyar ra’ayoyi kan mahimman ayyukan ci gaba da aka yi a wasu kasashe ta yadda za su iya zam wa kyaukyawan musali ga wasu. 

Kungiyoyin fararan hulla masu rajin kare dimukuradiyya da suka halarci taron sun yi batutuwa masu armashi da ka iya zama kyaukyawan musali ga sauran kasashen Afirka wanda ya kunshi ko baya ga mika mulki salin alun ba tare da wata hatsaniya ba, karfafa tsarin da dimukuradiyya don ci gaban jama'a da bai wa al'umma romonta.