1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Tattaunawa kan zaman lafiya

November 8, 2018

Zaman tattaunawa kan hanyoyin tabbatar zaman lafiya da Gidauniyar Konrad Adenauer ta Jamus ta jogoranta a garin Kaduna na Najeriya da bangarorin jama'a.

https://p.dw.com/p/37t7x
Nigeria - Kanduna
Hoto: Getty Images

Gidauniyar Konrad Adenauer ta Jamus ta gudanar da wani taron da ya hada kan malaman adini da masu rike da sarautun gargajiya wanda kuma ya mayar da hankali kan bunkasa zaman lafiya tsakanin mabiya addinai dabam-dabam a jihar ta Kaduna.

Gidauniyar Konrad Adenauer ta yi imanin amfani da malaman addinai da masu ruwa da tsaki za su taimaka wajen ganin samar da zaman lafiya tsakanin mutane masu addinai dabam-dabam da al'adu dabam-dabam. Lokacin zaman taron an tattauna kan batutuwa masu yawa da suke hana zaman lafiya da matakan da za su taimaka na zaman lafiya tsakanin jama'a.