haramcin takara ga magoya bayan Blaise Compaore
April 8, 2015Talla
A kan waɗannan sauye-sauye gwamnatin ta haramta wa magoya bayan tsohon shugaban ƙasar wato Blaise Compoare tsayawa takara a zaɓuɓɓukan da za a gudanar a ƙasar.
Hakan kuwa ya biyo bayan da majalisar dokokin ƙasar ta kaɗa ƙuria'r amincewa da daftarin ƙudirin wanda gwamnatin ta gabatar da shi a gareta. A cikin watanni na gaba da ke tafe ne za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da na 'yan majalisu a Burkina Faso.