1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare a Brussels

Kamaluddeen SaniMarch 22, 2016

An samu fashewar bama-bamai a Brussels hedkwatar Kungiyar Tarayyar Turai inda yanzu haka aka rufe tashoshin jiragen sama da na kasa har zuwa wani lokaci.

https://p.dw.com/p/1IHW4
Belgien Brüssel Innenstadt Metro Station Maelbeek Feuerwehr
Hoto: picture-alliance/AP/APTN

Hukumomin kasashen Turai sun kara tsaurara matakan tsaro a filayen tashi da saukar jiragen sama da tintunan kasashen, su bayan wani mumunan hari da aka kai a filin tashin jiragen saman Brussels da tashar jiragen kasa.

Kawo lokacin rubuta wannan labarin, a kalla mutane 34 suka mutu a yayin da wasu 170 suka sami raunuka, sakamakon harin kunar bakin wake da ya shafi zauren tashin fansinjojin filin jirgin sama da kuma wani harin da aka kai a tashar jiragen karkashin kasa duk dai a birnin na Brussels a safiyar yau.

Hukumomin gudanarwar filin jirgin saman birnin Brussels suka ce tuni aka fara gudanar da bincike, a yayin da kasashen Britaniya da Portugal suka kira wani taron gaggawa bayan daukar matakan tsaro a filayen jiragen saman kasashensu.

Kazalika mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida kasar Ostiriya, Karl-Heinz Grundboeck, shi ma ya ce tuni kasar ta baza 'yan sanda a kan titunan filayen jirgin sama da tashoshin jiragen kasa a Vienna babban birnin kasar gami da wasu manyan biranen kasar.

Suma hukumomi a kasar Jamus sun dauki irin wadannan matakan domin kare lafiya da dukiyoyin jama'a.