Hare-hare a garin Gao na kasar Mali
October 7, 2013Mai magana da yawun rundunar hadin gwiwa ta sojin Mali da Faransa wanda suka yi aiki fatattakar masu kaifin kishin addini a Mali din ya ce garin Gao da ke arewacin kasar ya fuskancin hare-hare na bam a karon farko cikin watanni da dama.
Jami'in mai suna Hubert de Quievrecourt ya ce kimanin bam biyar aka jefa da sanyin safiyar yau a garin na Gao wanda biyu daga cikinsu suka fada wata unguwa ta fararen hula.
Kawo yanzu dai babu wani wani labarin asarar rayuka da aka samu sai dai mai Mr. Quievrecourt ya ce sojan gwamnatin Mali daya ya jikkata.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai harin sai dai mabiya kungiyar nan ta Al-Qaida a watannin da suka gabata sun karbe iko da garin kafi daga bisani a fatatake su.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe