1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare gabannin zabe a Nijer

Yusuf BalaMarch 18, 2016

'Yan bindigar da suka kai harin dai ana saran sun kasance mambobi ne na kungiyar Al'Qaeda reshen AQIM.

https://p.dw.com/p/1IFZm
Nigeria Soldaten Archiv 2013
Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Wasu tagwayen hare-hare sun yi sanadi na kisan 'yan sanda uku da soja daya a ranar Alhamis a jamhuriyar Nijer, kamar yadda jami'ai suka bayyana, harin da ke zuwa kwanaki gabanin a gudanar da zaben shugaban kasa zagay na biyu.

'Yan bindigar da suka kai harin dai ana saran sun kasance mambobi ne na kungiyar Al'Qaeda reshen AQIM sun kuma harbe 'yan sandan uku a wata kasuwa ta Dolbel da ke a iyaka da Burkina Faso kamar yadda ministan cikin gida Hassimi Massaoudou ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP. A cewar ministan an maida wa 'yan ta'addar martani inda suka kwashe wadanda aka kashe daga bangarensu da ma wadanda suka sami raunika.

Kusa da iyaka da Najeriya ma wasu 'yan kunar bakin waken hudu sun kai wa jerin gwanon motocin soja hari a cewar minista Massaoudou, lamarin da yayi sanadi na kwamandan soja daya a yankin da raunata wasu guda biyu. Har ila yau ya kara da cewa an kuma samu dama ta hana wata yarinya ta biyar sanye da jigidar bam tashin nata bam din. Babu dai wani da abin ya shafa daga bangaren farar hula.