1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare kan masu sha'awar kwallon kafa

June 20, 2014

Masu ta da kayar baya a Najeriya sun mayar da hankali kan kai hari a kan 'yan kasa da ke sha'awar wasan kwallon kafa da ke da muhimmanci ga mafi yawan 'yan kasar.

https://p.dw.com/p/1CMMh
Nigeria Boko Harem Selbstmordattentat WM Public Viewing Damaturu
Hoto: STR/AFP/Getty Images

Bari mu fara da jaridar Die Tageszeitung wadda a labarinta mai taken hari a kan abin da 'yan kasa ke sha'awa ta mayar da hankali kan hare-haren da ake kaiwa kan gidajen kallon kwallon kafa a Najeriya.

Ta ce mutane da yawan ne suka rasa rayukansu sannan da dama suka jikkata a harin da aka kai kan wani gidan kallon kwallon kafa a Damuturu ta jihar Yobe lokacin wasan kwallon kafar duniya tsakanin Brazil da Mexiko. Hakan da na saka tsoro a zukatan mutane, musamman kasancewa wasan kwallon kafa na taka muhimmiyar rawa a tsakanin al'ummomin tarayyar Najeriya da ke fama da bambamce-bambamcen kabilanci, addini, yanki da kuma al'adu. Da ma dai tun gabanin fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya kungiyar Boko Haram ta kai hare-hare. Na farko a kan wani gidan kallo a garin Jos lokacin wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar Turai wato Champions League. Sannan kimanin makonni biyu da suka wuce an samu fashewar bam a lokacin wasan kwallon kafa a Mubi da ke jihar Adamawa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 40.

Amincewa da 'yan Afirka masu horas da 'yan wasa

Ita ma jaridar Berliner Zeitung tsokaci ta yi kan wasan kwallon kafar musamman masu horas da 'yan wasa 'yan Afirka.

Interaktiver WM-Check 2014 Trainer Nigeria Keshi
Stephen KeshiHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Ta ce coachin Najeriya Stephen Keshi ya aza ayar tambaya cewa mai yasa ake da karancin 'yan Afirka masu horas da 'yan wasa? Ta ce ba a bukatar yin wani dogon nazari kafin gano amsar wannan tambaya. Keshi daya daga cikin 'yan Afirka kalilan da ke horas da 'yan wasan kwallon kafa da suka yi nasara ya sha korafin cewa ba ya samun amincewar da yake bukata, kana Najeriya da kanta na yi wa harkar kwallon kafarta zagon kasa. Jaridar ta kara da cewa masu sukar lamirin Keshi sun ga yadda yake gwagwarmayar ci gaba da gudanar da aikinsa, bayan kokarin da aka yi sau da yawa na maye gurbinsa da wani coachi daga Turai. Keshi din dai na mai ra'ayin cewa idan aka ba wa 'yan Afirka goyon bayan da suke bukata to za su taka muhimmiyar rawa kuma ai ba bu wani abin da coachi daga Turai zai yi da 'yan Afirka ba za su iya yi ba.

Harkar bude ido ta samu koma baya a Kenya

Hari a gabar tekun Kenya inji jaridar Süddeutsche Zeitung sanda take tsokaci ga harin ta'addanci da aka kai kan wasu otel-otel da ke yankin Mpeketoni inda aka hallaka mutane 49.

Kenia - Anschlag der al-Shabaab-Miliz
Harin da al-Shabaab ta kai a KenyaHoto: picture-alliance/dpa

Ta ce a kwanakin nan kasar Kenya na fuskantar hare-hare da ake zargin kungiyar Al-Shabaab da hannu. Wannan lamarin ya shafi fannin yawon bude ido da ke da muhimmanci wajen samar wa kasar ta Kenya kudaden shiga. A cikin watan Satumban bara mutane 69 suka mutu a harin da kungiyar Al-Shabaab ta kai kan rukunin kantuna a cibiyar kasuwanci ta Westgate da ke Nairobi. A halin da ake ciki 'yan sandar Kenya sun tsaurara matakan tsaro a fadin kasar, kasancewa yanzu lokaci ne da masu yawon bude ido daga kasashen Turai ke kwarara kasar. Tun wasu makonni da suka wuce kasashen yamma ciki har da Jamus da Birtaniya suka gargadi 'yan kasashensu da su guji zuwa birnin Mombasa da gabar teku a kudanci da kuma arewacin kasar ta Kenya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe