1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare sun yawaita a gidajen kallon kwallo a Najeriya

June 18, 2014

Rundunar 'yan sanda ta bukaci hadin kan 'yan Najeriya wajen kawar da hare-hare a gidajen kallon kwallo, bayan da bam ya hallaka kimanin mutane 15 a gidan kallon kwallo da ke garin Damaturu na Yobe.

https://p.dw.com/p/1CLZV
Hoto: picture alliance/augenklick

Ana ci gaba da mayar da martani bayan da bam ya hallaka kimanin mutane 15 a gidan kwallon kwallo da ke garin Damaturu fadar gwamnatin Jihar Yobe da ke yankin Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya. Mutane 15 27 ne suka samu raunuka, a sanadiyar wani bam da ya tarwatse a filin kalon kwallo da ke garin Damaturu na jihar Yobe na Najeriya. Wannan ya auku ne lokacin wasan da Brazil ta kara Mexico don neman lashe kofin duniya na kwallo kafa.

Tuni dai rundunonin 'yan sanda na jihohin arewacin Najeriya suka dauki matakan gargadi ga masu gigan kallo kwallo. DSP Haruna Mohamed na Bauci ya bukaci al'umma da su "bayar da hadin kan dangane da duk abubuwan da ba su yarda da su ba, ko kuma mutanen da ba su amince da su ba."

Public Viewing in Accra Ghana Fußball WM 2014
Hoto: Mariam Sissy

Jami'an 'yan sandan suka ce za su sa ido a sauran guraren da ake da cunkoson jama'a a arewacin Najeriya don kawar da barazanar kai hare-hare. Da ma dai gwamnatocin jihohin Adamawa da Plateau sun haramta kallon kwallon kafa a gidajen kallo bisa dalilai na tsaro.

Idan dai za a iya tunawa, an kai hare-hare a wasu sassa na arewacin najeriya gabanin shirye-shiryen kofin duniya na kwalon kafa da ke gudana a kasar Brazil.

Mawallafi: Ardo Abdullahi Hazzad
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe