1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Boko Haram a Nijar da Kamaru

February 9, 2015

Mayakan Boko Haram sun kai harin bam a kusa da wani ofishin hukumar kwasta a Diffa yayin da a Kamaru suka farma wasu garuruwa guda uku.

https://p.dw.com/p/1EYmr

Wani bam ya fashe a garin Diffa da ke kan iyakar Nijar da Najeriya, sa'o'i kadan bayan Boko Haram ta kai hari kan wani gidan kurkukun garin. Wata majiyar soja a Diffa ta ce an dana bam din ne cikin wata mota, kuma harin ya janyo asarar rayuka da jikkata wasu da dama. Shaidun ganin ido sun ce an kai harin ne kusa da ofishin hukumar kwasta. Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da 'yan majalisar dokokin Nijar ke kada kuri'ar amincewa da shigar da kasarsu cikin kawancen dakarun kasashen yanki don yakar Boko Haram.

A can Kamaru kuwa rahotanni sun ce mayakan Boko Haram sun kai hare-hare kan wasu garuruwa uku inda suka yi garkuwa da akalla mutane 30 ciki har da fasinjojin wata bas. A garin Koza da ke arewacin Kamaru Boko Haram ta sace mutane 20 da ke cikin motar bas din, sannan sun kai hari a garin Kolofata inda suka sace abinci da dabbobi.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Suleiman Babayo