1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-Haren ta'addanci a Iraƙi

January 12, 2014

Wasu tagwayen hare-hare da aka kai a sassa daban-daban na Bagadaza babban birnin kasar Iraƙi sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla fararen hula 13.

https://p.dw.com/p/1ApLN
Hoto: Reuters

Hare-haren dai sun kuma yi sanadiyyar jikkata wasu mutane da dama, kuma wannan zub da jini na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da bata kashi tsakanin jami'an tsaron ƙasar da kuma mayaƙan 'yan tawaye dake da alaƙa da ƙungiyar Al-Qa'aida a gundumar Anbar, wani yunƙuri da sojojin suke na fatattakar masu tsastsauran ra'ayin.

Hari mafi muni dai an kai shi ne a tashar motoci da ke tsakiyar birnin na Bagadaza inda mutane tara suka hallaka yayin da wasu 16 suka samu raunuka, hari na biyu kuma da aka kai da wata mota ya afku ne a garin Hurriyah da ke arewacin Bagadaza tare da hallaka mutane hudu yayin da wasu 12 suka jkkata.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane