1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Taliban a Pakistan

August 15, 2014

'Yan kungiyar Taliban na ci gaba da kai hare-hare a kasar Pakistan a wani mataki da ke haddasa fargaba ta rashin tsaro a tsakanin al'ummar kasar.

https://p.dw.com/p/1CvY9
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Kungiyar Taliban reshen kasar Pakistan ta ce ita ce ke da alhakin kai wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar 'ya'yan kungiyar 12. Wasu gungun 'yan bindiga ne dai dauke da makamai da jigidar boma-bomai domin kai harin kunar bakin wake suka tinkari sansanin rundunar mayakan saman Pakistan din da ke Samungli da kuma sansanin sojoji na Khalid wanda dukkansu ke garin Quetta babban birnin gundumar Baluchistan. Bayan kwashe sama da sa'oi tara ana fafatwa tsakanin dakarun kasar ta Pakistan da kuma maharan, dakarun gwamnatin sun samu nasarar fatattakar maharan inda 12 daga cikinsu suka sheka barzahu. A baya-bayan nan dai kasar pakistan na fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyar ta Taliban akai-akai.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu