1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari kan jami'an Majalisar Dinkin Duniya

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 1, 2017

Wasu gungun mutane dauke da makamai sun kai hari kan wasu jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a garin Kontcha wanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

https://p.dw.com/p/2WoYC
Harin ta'addanci a kan iyakar Najeriya da Kamaru
Harin ta'addanci a kan iyakar Najeriya da KamaruHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Rahotanni sun nunar da cewar 'yan bindigar sun kai harin ne a ranar Talata 31 ga watan Janairun da ya gabata, da misalin karfe biyu na rana agogon Najeriyar da Kamaru. Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da yankin yammacin Afirka da ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya sanar da cewar daga cikin mutanen da harin ya rutsa da su akwai wani jami'in Majlisar Dinkin Duniyar da kuma 'yan Najeriya uku da dan Kamaru guda daya. Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ya dauki alhakin harin, sai dai dama yankin ya saba da hare-haren Kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram da ke gwagawarmaya da makamai a Najeriya da wasu makwabtanta.