1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari kan makarantar MDD a Gaza ya kashe mutane 10

August 3, 2014

Kimanin mutane 35 ne dai suka jikkata daga wannan hari, wanda Isra'ila ta ce tana gudanar da bincike a kansa.

https://p.dw.com/p/1Co5Q
Nahostkonflikt Angriff auf UN-Schule in Rafah 3.8.2014
Hoto: SAID KHATIB/AFP/Getty Images

Harin bam na sojin Isra'ila a makarantar Majalisar Dinkin Duniya inda Falasdinawa ke samun mafaka a Gaza ya kashe mutane da yawa. A yanzu haka wadanda suka samu raunuka na karbar jinya a asibitin A Najjar da ke yankin. Saleh al- Homs shi ne shugaban jami'an jinya na asibiti:

"A lokaci daya kawai sai muka ji cewar an kai hari kan makarantar MDD, daga nan kuma sai ga gawarwakin mutane da wadanda suka jikkata. Muna jinyar wasu a nan asibitin, a yayin da wadanda ba zamu iya ba, mun turasu wani asibiti da ke kusa da mu".

Rundunar Sojin Isra'ila ta ce tana binciken wannan hari, wanda ke zama irinsa na biyu a kan makarantar a kasa da mako guda. Hotunan Talabijin na kampanin dillancin labarai na Reuters ya nuna yadda tankunan yakin Isra'ila da sojojinta suka fara ficewa daga yankin. Duk da cewar kakakin rundunar sojin Bani Yahudun bai ce sun janye kenan ba, an fadawa mazauna unguwannin Falasdinawa da ke kewayen cewar, akwai yiwuwar dawowarsu.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu