1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Amirka a Pakistan

January 16, 2006

Harin da Amirka ta kai a wani kauyen Pakistan da nufin halakad da mataimakin shugaban kungiyar al-Qaeda, Aiyman al-Zawahiri dai bai sami nasarar cim ma burinsa ba. Sai dai, fararen hula 18 sun rasa rayukansu, abin da kuma ya janyo fusata da bacin ran dubban jama'an kasar ta Pakistan

https://p.dw.com/p/Bu2P
Ayman al-Zawahiri, mataimakin shugaban kungiyar al-Qaeda, wanda Amirka ke neman halakawa.
Ayman al-Zawahiri, mataimakin shugaban kungiyar al-Qaeda, wanda Amirka ke neman halakawa.Hoto: dpa

Bisa dukkan alamu dai, gwamnatin Pakistan ma ba sane take ba, da harin da Amirka ta kai a arewa maso gabashin iyakar kasar da Afghanistan. Da yake amsa tambayoyin maneman labarai, ministan sadaswa na kasar Pakistan din, Sheikh Rashid Ahmed, ya bayyana cewa:-

„Abin da zan iya fada yanzu shi ne, muna gudanad da bincike, don mu tabbatar cewa ko an kashe wani rikakken dan ta’adda a yankin ko kuma a’a. Sai bayan an kammala binciken ne zan iya ba da sanarwa.“

Da aka dage dai kan sai ya bayyana matsayin Pakistan game da harin, ministan cewa ya yi:-

„Na dai fada muku duk abin da zan iya fada yanzu, wato cewa, muna Allah wadai game da wannan matakin. Shi ke nan.“

Matakin da minista Rashid Ahmed ke nufi a nan dai, shi ne harin rokoki da jiragen saman Amirka suka kai a kan kauyen Damadola, wanda ke kan iyakar Pakistan din da Afghanistan, a ran juma’ar da ta wuce, inda mutane 18 suka rasa rayukansu, a cikinsu har da yara kanana guda 5. A halin yanzu dai, rokokin sun ragargaza kauyen gaba daya. Su dai Amirkawan, sun tanadi halaka mataimakin shugaban kungiyar al-Qaeda ne Eiman al-Zawahiri. Amma bisa rahotannin da gwamnatin Pakistan din ta bayar, shi al-Zawahirin, ba ya cikin mutanen da suka rasa rayukansu a harin.

Kawo yanzu dai, Amirka ba ta ce uffan ba tukuna game da harin. Sai dai, wasu kafofin kungiyoyin leken asiri sun ce, jiragen saman Amirka, sun harba rokoki a kan kauyen ne, saboda labarin da kungiyar leken asirin Amirkan, wato CIA ta samu na cewa, al-Zawahhiri na wani taro da shugabannin kungiyar al-Qaeda a kauyen.

Gwamnatin Pakistan ta mika wa jakadan Amirka a birnin Islamabad takardar nuna adawa da bacin ranta ga harin, bisa manufa. Dubban jama’a kuma sun yi zanga-zangar nuna bacin ransu da kuma yin Allah wadai ga harin, a babban birnin jihar wannan yankin, wato Khar. A halin da ake ciki dai, za a iya cewa, shugaba Musharraf ya sami kansa cikin wani mawuyacin hali. Saboda duk masu kishin islama a kasar na ganin cewa, shugaban ya wuce gona da iri, a hadin kan da yake bai wa Amirka, a fafutukar da take yi wai na yakan ta’addanci.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Amirka ta yunkuri halakad da al-Zawahiri ba. A shekaru 8 da suka wuce ma, bayan hare-haren da aka kai a kan ofisoshin jakadancin Amirka a Kenya da Tanzaniya, rundunar sojin Amirkan ta mai da martani da kai wa sansanonin horad da mayakan kungiyar al-Qaeda a kasar Afghanistan. A wannan lokacin dai, an yi zaton cewa, Usama bin Laden da al-Zawahiri na cikin sansanonin. Sai dai sun tsira daga hare-haren ba tare da ko kusa ta karce musu jiki ba.