1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Ansbach na da alaka da Kungiyar IS

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 25, 2016

Ministan cikin gida na Jihar Bavaria Joachim Hermann shi ne ya tabbatar da wannan labari a wani sabon taron manema labarai da ya yi.

https://p.dw.com/p/1JVae
Selbstmordanschlag Ansbach Bayern Absperrung
Hoto: picture-alliance/dpa/K.J.Hildenbrand

Jami'an tsaro da masu gabatar da kara a Jamus na ci gaba da gudanar da binicke domin gano dalilin da ya sanya aka kai wasu jerin hare-hare a kasar a karshen mako, abin da ya tsunudma mazauna kasar cikin halin rudani musamman ma a jihar Bavaria da ke yankin kudancin kasar.

Hare-Hare-guda hudu a cikin lokaci kankane

Kama daga harin da matashin nan dan shekaru 18 da haihuwa ya kai da bindiga tare da hallaka mutane tara kafin daga bisani ya harbe kansa a birnin Munich na jihar Bavaria, da kuma na wani da ya kai da adda a wani gidan cin abinci a birnin Reutlingen da ke yankin Kudu maso Yamamcin kasar, inda ya hallaka mace guda tare da raunata wasu mutane biyar, sai kuma na wani dan kunar bakin wake da ya tashi abubuwa masu fashewa da yake tare da su a birnin Ansbach duk dai a jihar ta Bavaria, yayin bukukuwan kade-kade da raye-raye, inda ya hallaka kansa da kansa tare da raunata mutane 12. Yanzu dai abin damuwa shi ne yadda kowa ke cikin fargabar halin da zai iya tsintar kanasa a ciki, ko da yake a jawabin da ta gudanar ga manema labarai a ranar Asabar din karshen mako, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta nunar da cewar ta fahimci yadda al'umma ke da fargaba da kuma tunane-tunane daban-daban kan halin da kasar ta tsinci kanta a ciki, sai dai hakan ba yana nufin za a dora alhakin wadannan hare-hare ga dukkanin 'yan gudun hijirar da suka shigo Jamus ba. Rahotannin dai sun nunar da cewar mutumin da ya kai hari na karshe inda ya hallaka kansa yayin da yake dauke da abubuwa masu fashewa a birnin Ansbach cikin daren Lahadin da ta gabata, dan asalin kasar Siriya ne mai kimanin shekaru 27 da haihuwa, kana ya taba yunkurin kashe kansa yayin kuma da rahotannin baya-bayan nan ke nuni da cewa an ma bayar da takardar mayar da shi zuwa kasarsa wato Siriya har sau biyu. Da yake ganawa da manema labarai kan batun takardar mayar da mutumin zuwa Siriya, kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida ta Jamus din Dr. Tobias Plate,cewa ya yi:

Deutschland Ansbach Explosion Pressekonferenz Innenminister von Bayern Joachim Herrmann
Joachim Herrmann ministan cikin gida na Jihar BavariaHoto: picture-alliance/dpa/D. Karmann

"Gaskiyya ne cewa ba za a iya mayar da 'yan Siriya zuwa gida a halin da ake ciki yanzu ba, wannan baya daga cikin abin da za a mayar da hankali a kansa, sai dai hakan ba yana nufin ba za a iya mayar da 'yan Siriya gida kwata-kwata ba. Wannan matsalar ta shafi dan Siriya ne wanda muka san an bayar da umurnin a mayar da shi, amma zuwa Bulgeria."

Matashin da ya kai harin Ansbach dan Siriya ne

Shi dai wannan matashi na daga cikin 'yan kasar Siriyan 500 da ke neman mafaka a Jamus wadanda kuma ke zaune a wani gida da aka tanadar musu a birnin na Ansbach, kana wadanda suka sanshi sun bayyanashi a matsayin mutumin kirki mai kuma son jama'a. Da yake jawabi ga manema labarai, ministan cikin gida na jihar ta Bavaria Joachim Herman ya bayyana cewar 'yan sanda sun sanshi.

Bayern Ansbach Selbstmordanschlag Ermittlungen Spurensicherung Polizei
Hoto: Reuters/M.Rehle

"Wanda ake zargi da tayar da abubuwa masu fashewar, ya sha zuwa wajen 'yan sanda a matsayin mai laifi. Kana takaddunsa da ke hannunmu sun nunar da cewar ya yi yunkurin hallaka kansa har sau biyu, wanda hakan ce ta sanya ake kula da shi a asibitin masu tabin hankali da ke birnin."

Daga cikin hare-hare hudu da aka kai a Jamus din dai cikin mako guda, maharan uku sun mutu, yayin da jami'an 'yan sanda suka yi nasarar cafke wanda ya kai hari da adda a birnin Reutlingen na Kudu maso Yammacin Jamus din tare da hallaka mace guda da kuma raunata wasu mutane biyar.