1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Bam ya halaka rayuka a Najeriya

October 30, 2017

Wani dan kunar bakin wake ya halaka mutane akalla 5 tare da jikkata wasu da dama, a wani hari da ya kai kauyen Ajiri Yala da ke arewacin birnin Maiduguri na jihar Borno.

https://p.dw.com/p/2mkZL
Nigeria Boko Haram - Kinder als Selbstmordattentäter
Hoto: picture-alliancce/AP Photo/J. Ola

Rahotanni daga Najeriya na cewa wani dan kunar bakin wake ya halaka mutane akalla 5 tare da jikkata wasu da dama, a wani hari da ya kai kauyen Ajiri Yala da ke arewacin birnin Maiduguri na jihar Borno. Kamar dai yadda wani dan Kato-da-Gora ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP, maharin ya saje ne da masallata cikin wani masallaci yayin sallar Asuba. Ko a Lahadin da ta gabata ma wani dan Kato-da-Goran ya rasa ransa a wani shingen binciken da ke yankin Muna a birnin Maiduguri, lokacin da wasu 'yan mata masu bama-bamai suka tarwatsa kansu.

Wasu bayanan da ke fitowa daga yankin Gulak na karamar hukumar Madagali a arewacin jihar Adamawa ma dai na cewa wasu 'yan matan biyu da aka yi zargin sun fito ne daga sansanin Sambisa, sun tarwatsa kansu a kauyen Dar, sai dai babu labarin mutuwar wani ko samun rauni.