1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya kashe sojojin Chadi a Mali

Binta Aliyu Zurmi
April 16, 2021

Wasu jami'an soji biyu na rundunar sojojin yankin tafkin Chadi sun rasa rayukansu a Mali bayan da motarsu ta taka wani bam da mayakan jihadi suka dana.

https://p.dw.com/p/3s6AM
Burkina Faso Franzöische Soldaten Operation Barkhane
Hoto: Philippe De Poulpiquet/MAXPPP/dpa/picture alliance


Harin ya auku ne a yankin Boulkessi, yankin da kungiyar Serma Katiba da ke da alaka da Al-Qaeda ke gudanar da ayyukanta a kasar Mali. Sojojin biyu na kasashen Chadi ne a cewar sanarwar da mai wakiltar Majalisar Dinkin Duniya a Mali Mahamat Saleh ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

A yankin na Tafkin Chadi dai akwai rundunoni da dama da suke yaki da mayakan da ke gwagwarmaya da makamai ciki kuwa har da  rundunar sojin Faransa ta Barkhane.