1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya hallaka mutane 70 a birnin Bagadaza

Mohammad Nasiru AwalAugust 13, 2015

'Yan tarzomar kungiyar masu kaifin kishin addini ta IS sun dauki alhakin kai harin a cikin wani sako da suka wallafa a shafin intanet.

https://p.dw.com/p/1GFBR
Irak Bombenanschlag in Bagdad
Hoto: Reuters/W. Al- Okili

Akalla mutane 70 sun rasu sannan fiye da 200 sun samu raunuka a wani harin bam da aka kai kan wata babbar kasuwa da ke Bagadaza babban birnin kasar Iraki. Tuni 'yan tarzomar kungiyar masu kaifin kishin addini ta IS suka dauki alhakin kai harin a cikin wani sako da suka wallafa a shafin intanet. Harin da ya auku a unguwar Sadr Cita ta 'yan Shi'a an kai ne a kan sojoji da masu mara musu baya a unguwar. Da farko 'yan sanda sun ba da sanarwar fashewar wata babbar mota makare da bam a kasuwar wannan unguwa. Harin dai na daya daga mafiya muni tun bayan da Firaminista Haider al-Abadi ya karbi ragamar mukamin shugaban gwamnati shekara guda da ta wuce.