1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan ta fuskanci harin ta'addanci

January 20, 2016

Wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota a daf da ofishin jakadancin Rasha da ke Kabul babban birnin kasar Afghanistan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai.

https://p.dw.com/p/1HhPn
Harin ta'addanci a Afghanistan
Harin ta'addanci a AfghanistanHoto: Reuters/O. Sobhani

Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida ta Afghanistan din Sediq Sediqi, ya sanar da cewa jami'an 'yan sanda na kokarin tan-tance mutanen da harin ya rutsa da su. Shima kakakin ma'aikatar lafiya ta kasar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin Mohammad Ismail Kawusi ya shaidar da cewa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai mata uku da wani namiji guda. Shugaban 'yan sandan birnin kabul Abdul Rahman Rahimi da ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce:

 

"Dan kunar bakin wake cikin mota kirar Toyoya Corolla ne ya kai harin. Ya daki motar wani gidan talabijin ne. Kawo yanzu mutane bakwai da suka hadar da mata biyu sun yi shahada, kana wasu 25 sun jikkata."

Mutanen bakwai da suka rasa rayukansu dai ma'aikatan gidan talabijin na TOLO na kasar ta Afghanistan ne. Ofishin jakadancin Rashan dai da ke Kabul ya sanar da cewa babu wani jami'insa da harin ya rutsa da shi.