1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ta'addanci kan sojin Mali

Ahmed SalisuSeptember 10, 2016

Ma'aikatar tsaron Mali ta ce wasu sojin kasar uku sun rasa ransu yayin da wasu biyu suka ji raunuka sakamakon hari da aka kai musu birnin Boni da ke tsakiyar kasar.

https://p.dw.com/p/1Jznh
Mali Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/J. Saget

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron tafidda dazu ta ce 'yan bindigar da suka hallaka sojin sun yi musu kwanton bauna ne lokacin da suke kokarin wucewa a kan hanyar da ta hada Douentza da Gao a lardin Mopti. Ya zuwa yanzu dai hukumomi a kasar ba su yi karin haske ba game da wannan hari kana ba wata kungiya da ta dau alhakin kai harin. Arewacin Mali dai na fama da tashin hankali musamman daga masu kaifin kishin addini wanda suka karbe iko da shi cikin cikin shekarar 2012 kafin daga bisani wata runduna da sojin Faransa ta jagoranta su maido da yankin karkashin ikon gwamnati.