1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin tashin bom a birnin Tel-Aviv na Isra'ila

November 21, 2012

A yayinda al'ummar birnin Tel-Aviv na Isara'ila ke cikin juyayin tashin wata bom da aka dana a wata mot,ayankunan zirin Gaza murna kawaio ake ta yi da harin

https://p.dw.com/p/16nHP
Hoto: Reuters

Rahotani daga birnin Kuddus na Isra'ila sun tabbatar da aukuwar wani harin tashin bom a wata motar supurin jama'a da aka kai a wannan safiya a birnin Tel-Aviv na kasar inda kimanin mutane 10 ne suka samu munayen raunika,to saidai babu wasu rahotanin da suka bayana adadin wadanda suka mutu. Wannan harin ya zo ne a daidai lokacin da sakateriyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton da sakteriyar majalisar dinkin duniya Ban ki-moon ke tautaunawa da hukumnomin Isra'ila a matakin neman tsagaita wuta a yakin da ake gobzawa da Isara'ila da palastinawan yankin gaza mako daya kenan. Jim kadan bayan bayana wannan sanarwar harin murana ta kece a yankunan Gaza,kamun daga bisani kungiyar Hamas ta bayana daukar alhakin harin.
A dai bangare hukumomin Iran sun kira kasashen laranawa da su bi sahunsu gurin taimakawa mayakan Gaza da makamai.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohamad Nasiru Awal