1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda na bincike kan harin wuka a Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 21, 2018

Bayan wani hari da wuka da aka kai a cikin motar Bus a birnin Lübeck da ke Schleswig-Holstein a arewacin Jamus, an aika sammaci ga wanda ake zargi da kai harin.

https://p.dw.com/p/31run
Harin wuka cikin mota kirar Bus a Jamus
Harin wuka cikin mota kirar Bus a JamusHoto: picture-alliance/dpa/M. Scholz

Mai shekaru 34 a duniya, an zarge shi da kokarin yin kisa da yin munanan raunuka ga mutane da kuma haddasa gobara da gangan da nufin raunata mutane. Maharin wanda har kawo yanzu bai ce komai kan dalilinsa na kai wannan harin ba, ya kunna wuta a jakarsa ta goyo a cikin motar kirar Bus da ke dauke da fasinjoji, kana ya yanki mutane 10 da wuka. Fasinjojin da ke cikin motar ne dai suka hada karfi wajen damke shi tare da mika shi ga jami'an 'yan sanda.