1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Nijar akalla 60 sun hallaka

Abdoulaye Mamane Amadou
December 11, 2019

Rahotanni daga yankin Inates da ke makwataka da Mali a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar a kalla sojojin kasar 60 a yayin wani harin ta'addancin da mayakan jihadi suka kai wani sansanin soja. 

https://p.dw.com/p/3Uekf
Symbolbild Anschlag auf Militärbasis in Mali
Hoto: picture-alliance/dpa/M. de Martignac

Wata majiyar tsaro ta sojan kasar ta  tabbatar da kai harin ne da manyan rokoki da wasu ababen fashewa ko da yake rahoatnnin sun ce fashewar wata tanka ta man fetur na daga cikin abubuwan da suka kara haddasa mutuwar sojojin.

A na sa bangare shugaban kasar ta Nijar Mahamadou Issoufou da ke halartar wani taron koli kan batun zaman lahiya a nahiyar Afirka a kasar Masar ya bannaya a shafinsa na Twitter da katse halartar taron domin komawa a gida.

A farakon wannan makon ne dai hukumomin kasar suka kara tsawaita wa'adin dokar tabaci da aka kakaba wa yankin har na tsawon watanni uku bisa dalilai na rashin tabbataccen tsaro.