1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiya ta samar da manhaja

Nasir Salisu Zango LMJ
March 17, 2021

Sa'ada Aliyu matashiya ce wacce bayan ta kammala karatunta, ba ta tsaya jiran aiki ba sai ma ta yi amfani da ilimin nata wajen kirkirar wata manhaja da za ta ringa fallasa wadanda suka aikata fyade.

https://p.dw.com/p/3qkhL
Nigeria Anti-Rape App
Matashiya Sa'ada Aliyu da ta samar da na'urar yaki da fyade, a jihar Kano da ke NajeriyaHoto: Nasir Salisu Zango/DW

Yanzu haka dai matashiya dai ta zama tauraruwa a yankin arewacin Najeriya, sakamakon kirkirar wannan manhaja. Sa'ada Aliyu na kiran manhajar mai fallasa wadanda suka aikata laifukan fyade da "Helpiyo." Manhajar na taimakon hukumomi da kungiyoyin da za su kai dauki ta hanyar fallasa masu wannan muguwar dabi'a. Haifaffiyar jihar Kano, Sa'ada Aliyu ta yi karatunta ne a fannin kimiyar Computer.

Bisa al'ada dai ba kasafai ake iya cimma nasara ba tare da kalubale ba, dan haka matashiyar ta bayyana cewa duk da tarin nasarori da ta cimma, ta kuma fuskanci wasu kalubale kan wannan manhaja. Haka kuma Sa'ada ta bayyana matukar takaici kan yadda ake aikata fyade ba tare da an bi wa wadanda aka yi wa hakkinsu ba. A karshe Sa'ada Aliyu ta zaburar da matasa kan su dukufa wajen amfani da iliminsu, domin samar da hanyoyin ci-gaba ga al'ummar su, tana mai cewa matasa sune kashin bayan kowacce alumma.