1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dogaro da kai: Ba nakasasshe sai kasasshe

October 16, 2019

HDM a jihar Taraba wani matashi mai sunan Abdulmumin Isiyaku Jauro da ya kasance gurgu ya rungumi sana'ar wanki da guga a maimakon yin bara a titi.

https://p.dw.com/p/3RNVo
Greenpeace Chemikalien in Kinderkleidung Symbolbild
A Najeriya wani gurgu ya kama sana'ar wanki da gugaHoto: picture-alliance/dpa

Ko menene ya bai wa matashi Abdulmumin Isiyaku Jauro sha'awar wannan sana'a? A cewarsa ya rungumi sana'ar ne domin ya tsira da mutumcinsa kuma ta taimaka masa gaya domin da ita yake daukar nauyin iyalinsa da ma wasu da ke bukatar tallafi.

Jauro ya nunar da cewa ya kai sama da shekaru 10 yana wannan sana'ar kuma ya horar da matasa da dama masu lafiya da ba su da bukata ta musamman. Ya kuma yi kira ga 'yan uwansa masu bukata ta musamman da su yi watsi da bara, su zo su rungumi sana'o'i domin dogaro da kansu. Ya nunar da cewa duk da dimbin kalubalen da yake samu ta fuskacin sana'ar tasa ta yadda a lokuta da dama 'ya'yansa ke masa shnaya kuma in zai yi wanki ko guga sai an dora shi a kan kujera ko tebur, ba zai taba yin kasa a gwiwa ba wajen tallafa rayuwarsa. Ya kuma bukaci da mahukunta su tallafa masa domin bunkasar sana'ar tasa da ma jiharsu ta Taraba baki daya.