1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gombe: Matashiya mai kayan makulashe

May 6, 2020

Malama Khadija Muhammad Gwani wata matashiya ce a Gombe da ta ajiye takardar shaidar kammala karatunta na digiri ta kuma rungumi sana'ar yin kuli-kuli da sauran kayan makulashe.

https://p.dw.com/p/3brxl
Kartoffelgericht
Hoto: picture-alliance/dpa/K.C. Alfred

Wannan matashiya dai ta zabi yin wannan sana'ar duk da cewa akwai da dama da ke ganinta a matsayin sana'ar tsofaffi da bai kamata mai shekaru, irin nata ya yi ba. To sai dai Khadija Muhammad Gwani ta yi watsi da duk irin wannan tunani, inda ta kama yin wannan sana'a tare da zamanantar da ita, ta yadda za ta ba da sha'awa da kuma samar da kasuwa a kuma samu riba.

Khadija dai na yin wannan sana'ar a cikin gidansu, kuma tana amfani da kafafen sada zumunta na zamani kamar WhatsApp da Instagram domin tallata abubuwan da ta ke sayarwa. A cewarta hakan na taimaka mata wajen samun kasuwa daidai gwargwado. To sai dai Khadija ta bayyana cewa duk da nasarorin da ta samu, akwai kalubale musamman ma na yadda mutane ke kallon masu sana'ar, inda wasu ke neman sare mata gwiwa.