1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiya mai yin kayan makulashe

January 6, 2021

Wata matashiya a jihar Sakkwato da ke Najeriya, ta rungumi sana'ar yin kayan kwalam da makulashe domin rufa wa kanta asiri.

https://p.dw.com/p/3naYy
DW-Beitrag Nigeria Sokoto Pastries
Hoto: Ma’awiyya Abubakar Sadiq/DW

Rukayya Abubakar Bajah matashiya ce da ke ajin karshe a jami'a, amma kuma ta rungumi sana'ar kayan makulashe, inda take yin gullisuwa da kwakumeti da carbin malam da makamantansu. Matashiyar dai ta rungumi sana'ar ne a wani mataki na  kaucewa rashin aikin yi da kuma dogaro da kai.

A cewar matashiya Rukayya Bajah ta samu alkhairi mai yawa sakamakon sana'ar tata, kuma tana daukewa kanta kudin makaranta da  sauran lalurorin yau da kullum, baya ga matasa da take koyawa sana'ar da kuma wadanda ke taimaka mata suke kuma cin abinci a karkashinta.