1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hira da Limamin Bangui

Usman ShehuFebruary 26, 2014

Shugabannin addinin Islama a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kawar da batun samun kungiyoyin 'yan ta'adda a rikicin kasar

https://p.dw.com/p/1BG6t
Porträt - Oumar Kobine Layama
Imam Oumar LayamaHoto: Getty Images

Kungiyoyi da dama ne da suka hada da AQMI, 'yan Taliban da kuma Boko Haram ake raderadin cewa sun ce za su kawo tallafi ga musulman Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ke cikin mayuwacin hali a yanzu.

Shugaban al'ummar musulmin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin wata hira da tashar DW ta yi da shi, ya ce iri-iren wadan nan kiraye-kiraye, batutuwa ne da ta kamata a dauke da muhimmanci, sannan a sanar cewa masu tsatsauran ra'ayi basu gama komai da koyarwa ta adinin Muslunci ba.

Batun kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, batu ne da ya dauki hankullan kasashe da dama harma da kungiyoyin adinnai, inda masu tsatsauran ra'ayi kamar su AQMI ta yankin Sahel, 'yan Taliban na Afghanistan da kuma Boko Haram ta Tarayyar Nageriya, ake batun cewa za su kawo dauki ga takwarorin su na kasa. A wata hira da DW Imam Oumar Layama shugaban kungiyoyin musulmai na kasar ta ya duba wannan batu tare da yi masa fassara.

Zentralafrikanische Republik Sangaris-Soldaten Polizist 09.02.2014
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Yace "Ni abun da zan ce kan wannan batu,ba yadda su suke so ba ne, mi ya sa na ce haka, domin halin da ake ciki a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ba matsala ba ce ta adini. Ba yaki ba ne na adini, yaki ne na soja da siyasa. Kasar faransa ta zo wannan kasa ne bayan da hukumomin wancan lokaci suka nemi zuwanta lokacin Michel Djotodia shugaban da yayi murabus. Ganin yadda kasar ta shiga wani yanayin da ya fi karfin su, ya sanya ya nemi agaji daga kasar Faransa domin ta taimaka a samu shawo kan matsalar, sannan kuma da dakarun kasashen Afirka na Minisca da suka zo"

Zentralafrikanische Republik Ausschreitungen Gewalt Christen Muslime 30.01.14
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

A cewar Imam Layama, akwai ma biranen da ake zaune lafiya tsakanin Kiristoci da musulmai, dan haka Kiristoci basu da matsala da musulmai. Wannan akida ta kisan jama'a akwai su daga kowane bangare na musulmai da kiristoci. Ni a matsayi na shugaban musulman wannan kasa, ina iya cewa wadan nan kiraye-kirayen basu da wani tushe kuma ba su cancanta ba.

Yayinda DW ta tambayi Imam Oumar Kobine Layama, ko baya gani bayannan da ake aikawa ta kafofin sadarwan zumunta na Internet, ba za su kasance wani babban hatsari na rura wutar rikici a wannan kasar ba, sai yace:

"Hakika, batutuwa ne da ta kamata a dauke su da muhimmanci, domin 'yan jaridu na kasashen waje da suka zo nan kasar sun ji ta bangaren wasu musulman, masu irin wannan niyya, inda ma suka ce nan ba da dadewa ba, za su samu makammai, cewa 'yan kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyi masu zafin kishin Islama, za su shigo cikin wannan kasar, lallai wannan batu na yawo a ko'ina tsakanin 'yan uwana musulmai na wannan kasar, ba zan iya boye hakan ba. Kokari zamu yi mu dukafa dan kwanciyar hankali ta dawo a wannan kasa, kuma dakarun kasashen wajan da ke wannan kasa, su ci-gaba da kare lafiyar al'umma ta yadda wadanda suka bar kasar cikin yanayi na tsoratarwa, su samu su dawo gida"

Afrika Gewalt in Bangui 29.01.2014
Hoto: AFP/Getty Images

Ganin cewa musulmai sune a matsayin 'yan tsiraru a wannan kasa ta tsakiyar Afirka, kuma ma akasari sune aka fi kai ma hari tare da kashe su a wani lokaci, ko mi Imam Layama zai ce da wannan yanayi da 'yan uwansa musulman suke ciki.

"Babban abun da ya dace da mu, na farko shi ne na mu tsaya tare, masu yi kishin wannan kasa, mu nemo mafita daga rikicin da ke addabar wannan kasa. Kuma ana iya cewa mu kan mu musulmai muna da namu laifi, domin kuwa a lokacin da 'yan Seleka suka yi ta kashe-kashen mutane lokacin suna mulki, indan da ace dukan limammai sun yi baki guda kamar yadda nake yi, sun yi kira ga 'yan Seleka da su daina wannan kashe-kashe, da yanzu bamu kai wannan matsayi ba".

To a halin yanzu ana iya jin tsoro ko shakku dangane da yiyuwar sa hannun kungiyoyin Aqmi ko Boko Haram a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ganin matsayin da rikicin ya kai.

"Dakarun da suka zo domin tsaron a wannan kasa dai sun ji wannan kira, dan haka na tabbata kuma na yi imani da cewa za su dauki matakan hana iri-iren wadan nan kungiyoyi samun wurin zama cikin wannan rikici. Domin idan har irin wadannan kungiyoyi suka shigo nan, to za'a samu mace-macen al'umma da dama a cikin anguwanni, kuma dalilin da zai kawo su nan ma ni ban ganshi ba, domin Allah na ya fada cikin Alkur'aninsa mai tsarki, cewa "babu tilastawa cikin addini" kuma ko da musulmai ne suke da rinjaye a wannan kasa, bazamu tilastawa kashi daya na kiristoci, cewa sai sun musulunta ba, kenan zamu barsu ne su yi addininsu"

Kan wannan batu dai na rikicin da wasu ke danganta shi da na addini, a cewa Limam Oumar Layama na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ai musulmai basu bin hanya ta gaskiya, sun sani kamar yadda Annabi ya yi a Madina, tare da dukkan al'adu, Kiristoci, musulmai, da ma wadanda basu da addini duk sun rayu tare babu tsangwama. Dan haka ban ga yadda a yanzu za'a rinka wani tunani da bai dace da adninmu ba, lallai hakan yana baiwa musulman da ke son aikata addinin su kan hanya ta gaskiya tsoro.

Mawallafa: Anne-Claude Martin/Salisou Boukari

Edita: Usman Shehu Usman