1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake dage sauraron karar Hissene Habre

Nura Datti Kan Karofi / LMJSeptember 7, 2015

Tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre ya kauracewa bayyana a gaban kuliya bisa tuhumarsa da laifukan yaki.

https://p.dw.com/p/1GSU2
Tsohon shugaban Chadi Hissene Habre
Tsohon shugaban Chadi Hissene HabreHoto: picture-alliance/dpa

Daga cikin laifukan da ake tuhumar tsohon shugaban kasar ta Chadi Hissene Habre da ake kwatanta shi da dan mulkin kama karya akwai na bayar da umarnin kisan mutane sama da 40,000 a zamanin mulkinsa a shekarar 1980. Idan dai za a iya tuna wa a watan Yuli ne aka dage shari'ar da ake yi masa bayan da Habre din ya bayyana kotun a matsayin haramtacciya tare da umartar lauyoyinsa da kada su halacci zaman kotun. Tun farko dai a zaman kotun na ranar Litinin din nan mai gabatar da kara a kotun kasar ta Senegal Mbacke Fall ya yi shelar cewar wanda ake tuhumar ba zai zo kotun ba, dan haka sai ya ce ya kamata kotun ta bada umarni da a tiso keyarsa sakamakon yadda ya bijirewa umarninta.

Zaman sauraron shari'ar Hissene Habre a Senegal
Zaman sauraron shari'ar Hissene Habre a SenegalHoto: picture-alliance/AP Photo/R. Blackwell

Sake dage sauraron kara Habre

Tuni dai Gberdao Gustave Kam dan kasar Burkina Faso da ke shugabantar wannan kotu ta musamman ta Afirka ya sake dage sauraren shari'ar da aka tsara yi a ranar Litinin din nan, batun da wasu ke ganin dama take-taken Habre sun nuna cewar ba zai ba da hadin kai ga kotun ba, kamar yadda wata 'yar jarida Celeste Hicks da ta gudanar da wani bincike a kansa da kuma yankin na Sahel ke cewa:

"'Yar manuniya ta nuna cewar da alama tsohon shugaban Chadi Hissene Habre ba zai bai wa kotun hadin kan da ya kamata ba, tun a lokacin da ya gurfana a gaban kuliya a watan Yulin da ya gabata, ganin yadda ya ki ya ce uffan game da tuhume-tuhumen da ake yi masa, kana kuma ya kekasa kasa yaki amincewa da alkalan da za su gudanar da shari'ar."

Shari'ar ba za ta gagara ba

To sai dai fa a cewar Celeste Hicks rashin bayyana Habre a gaban kuliya ya sagar wa da al'ummar da ake ganin tsohon Shugaban yaci zarafinsu gwiwa a kokarin su na ganin kotun ta kwato musu hakki, sai dai muddin kotun za ta dore a kan yadda ta jajirce, ba shakka akwai alamun burinsu zai iya cika.

'Yan sanda a gaban kotun da ke sauraron shari'ar Habre
'Yan sanda a gaban kotun da ke sauraron shari'ar HabreHoto: Getty Images/AFP/ Seyllou

Shima a nasa bangaren wani dan kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch Rid Brady, wanda ke bibbiyar shari'ar ya ce rashin bayyanarsa a kotun ba zai tsayar da shari'ar ba.

Yace: "Rashin zuwansa ba zai hana a yanke masa hukunci anan gaba ba, domin mutanen da ya zalunta ya zama dole shari'a ta yi aikinta ta kuma hukunta shi, don haka rashin zuwansa ba zai yi wani tasiri ba, hasalima shi ne zai tauye kansa ga damarsa ta bayar da ba'asi."

Shugaba Habre dai ya yi gudun hijira ne zuwa Senegal in da ake tuhumarsa da laifuffuka na take hakkin dan Adam a lokacin mulkinsa a shekarun 1982 zuwa 1990. Mai shekaru 72 a duniya Habre na samun goyan bayan kasashen Faransa da Amurka.