1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HRW: Ana tsare yara bisa yaki da ta'addanci

Mouhamadou Awal BalarabeJuly 28, 2016

Kungiyar HRW ta fidda sabon rahoto kan cin zarafin yara a kasashen da ke fama da tashin hankali, inda ta ce yaki da ta'addanci na sawa ana kama yaran da ba su ji ba.

https://p.dw.com/p/1JWyr
Human Rights Watch Logo

Kungiyar Human Right Watch ta bayyana cewar yaki da ake yi da Kungiyoyin 'yan ta'adda irinsu Boko haram da IS na sawa ana cin zarafin yara kanana a sassa daban-daban na duniya. Cikin wani sabon rahoton da ta wallafa a wannan Alhamis, kungiyar ta kasa da kasa ta ce yaran da ake tsare da su sun karu a kasashe shida da ke fama da tashin hankali ciki har da Najeriya da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da Afghanistan da Iraki da yankin Palesdinawa da Syriya.

A Syriya ga misali yara kusan dubu da 500 aka tsare a gidan yari a shekaru biyar da kasar ta shafe ta na fama da yakin basasa, 436 daga cikinsu ne kadai aka sako a cewar kungiyar. Rahoton na Human Right Watch ya zo ne kwanaki kalilan kafin wata muhawara da kwamitin sulhu na Majakisar Dinkin Duniya zai shirya a ranar Talata mai zuwa a kan halin da yara ke samun kansu a ciki a lokacin yaki.