1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomi a Najeriya sun kama miyagun kwayoyi

November 23, 2018

Hukumomi a Najeriya sun kama wasu miyagun kwayoyi masu yawan gaske da aka yi kokarin shiga da su cikin kasar daga ketare.

https://p.dw.com/p/38oFz
Lagos Port Hafen Nigeria
Hoto: AFP/Getty Images

A cewar hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama wasu sundukai 40 da ke shake da kwayoyin maganin nan na tramadol da wasu magunguna masu maye, kwayoyin da hukumar ta ce an shigo da su Najeriyar ne daga kasar Indiya.

Hukumar ta ce kwayoyin sun kai darajar kudin kasar na Naira sama da biliyan uku, da aka yi kokarin shiga da su kasar tashar jiragen ruwa da ke Legas.

Hakazalika, hukumar ta kuma kama wasu jirage masu saukar angulu guda biyu da aka yi kokarin shiga da su cikin kasar su ma cikin wasu sundukan da ba su da cikakkun takardu.

Kakakin hukumar ta Kwastam, Mr. Joseph Attah, ya ce an yi nasarar kamen ne bayan wasu bayanan sirrri ta hanyar hadin gwiwa da hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna wato NAFDAC.

Shugaban hukumar Kwastan ta Najeriyar, Kanal Haeed Ali, ya ce masu garkuwa da mutane da ‚yan ta’adda, su ne ke marmarin samun wadannan muyagun kwayoyin, don ci gaba da aikata muyagun kaba’iran da suka saba.

Ya kuma jaddada tsayuwar hukumar tasa wajen yaki da fasa-kwaurin haramtattun kayayyaki gami da sama wa Najeriyar kudaden shiga.