1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin tsaro sun nemi sulhu da Boko Haram

Usman ShehuJanuary 18, 2013

Rundunar jami'an leƙen asiri a Najeriya wato SSS, sun nemi ƙungiyar Boko Haram da ta shiga a yi sulhu don zaman lafiya

https://p.dw.com/p/17NGd
This image released by Saharareporters shows police and rescue workers after a large explosion struck the United Nations' main office in Nigeria's capital Abuja Friday Aug. 26, 2011, flattening one wing of the building and killing several people. A U.N. official in Geneva called it a bomb attack. The building, located in the same neighborhood as the U.S. embassy and other diplomatic posts in Abuja, had a huge hole punched in it. (Foto:Saharareporters/AP/dapd)
Rundunar jami'an tsaron Najeriya a AbujaHoto: dapd

Daraktan hukumar leken asiri ta SSS a jihar Borno Abdullahi Ahmed ya bayyana hakan a wani sako da aka aikewa manema labarai, ya bada dalilai da ya ce ya kamata jagororin Kungiyar su buda wajen kawo karshen wannan hare-hare da suke kaiwa a sassan najeriya. Wannan dalilai kuwa su ne kungiyar su duba Allah kuma su san cewa Allah baya kuskure da ya halicci Najeriya da kabilu da addinai mabambanta, su kuma duba yadda ake addinin Islama da suka ce domin kare shi su ke yi gami da duba halin dubban mata da yara da suka rasa mazaje da iyayen su gami da duba yadda yankin Arewa maso gabashin Najeriya ya shiga sanadiyyar wannan tashin hankali.

Wannan dai shine karo na farko da wata hukumar tsaro a Tarayyar Najeriya ta fito ta yi irin wannan roko abinda ya sa wasu ke ganin ko sun kasa magance matsalar ne suka koma yin wannan roko. Sai dai duk da haka al'umma sun yi marhabin da wannan mataki da suke ganin in an yi da gaskiya to kuwa za'a iya cimma sulhu kamar yadda Bala Jungudo Gombe ya shaida min.

epa03026909 Nigerian police control a street shortly after a bomb blast in a market in Ogbomoshoin area of Kaduna, Nigeria, 07 December 2011. Reports state the early morning explosion in the northern city of Kaduna killed 10 people, including a pregnant woman and two children. A group suspected to be Islamist militants reportedly arrived on motorbikes and threw bombs into the crowded spare parts market. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++
Wani harin da aka taɓa kaiwa a KadunaHoto: picture-alliance/dpa

A baya ma dai gwamnatin kasar ta yi kira ga ‘yan kungiyar da su fito su bayyana kan su don duba yadda za'a wanzr da zaman lafiya sai dai hakan ya bai yiwu ba saboda rashin sanin ‘yan Kungiyar inji hukumomin.

Wasu dai kamar Engr Sa'ad Abubakar Abdullahi na ganin wannan matakin kawai ba zai gamsar ba sai har Shugabannin a dukkanin matakai sun yi adalci ga mabiyan su. Yayinda hukumomin tsaron ke jaddada kira ga kira ga al'umma da su taimaka musu da da bayanai na wadanda ba su gamsu da su ba su kuma al'ummomin na dari-dari yin hakan saboda fargabar abinda ka iya biyo baya.

Smoke rises from the police headquarters as people run for safety in Nigeria's northern city of Kano January 20, 2012. At least six people were killed in a string of bomb blasts on Friday in Nigeria's second city Kano and the authorities imposed a curfew across the city, which has been plagued by an insurgency led by the Islamist sect Boko Haram. There was no immediate claim of responsibility for the apparently coordinated attacks. REUTERS/Stringer (NIGERIA - Tags: CRIME LAW CIVIL UNREST TPX IMAGES OF THE DAY)IL UNREST)
Wani harin da aka taɓa kaiwa a KanoHoto: Reuters

Sai dai Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Gombe Mataimakin Sufurtandan ‘yan sanda Fwaje Atajiri ya ce ya kamata mutane su dai na wannan fargaba. Hukumar tsaro ta SSS dai ta yi kira ga al'umma da su yi taka tsan-tsan da wasu ‘yan damfara da ke fakewa suna karbar kudade a hannun al'umma da sunan cewa su ‘yan kungiyar Boko haram ne wanda tace tuni ta kama wasu daga cikin su kuma ana shirin gurfanar da su gaban kuliya manta sabo.

Har ya zuwa lokacin da kamala wannan rahoto Kungiyar ta Jama'atu Ahlilsunna Lilda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ba su ce komai kan wannan roko da Hukumar SSS tayi ba.

Mawallafi: Amin Sulaiman Muhammed

Edta: Usman Shehu Usman