1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kisa kan dan adawa a Bangaladash

October 29, 2014

An yanke hukunci kisa wa daya daga cikin jiga-jigan 'yan adawan kasar Bangaladash

https://p.dw.com/p/1Ddzh
Hoto: AFP/Getty Images

Kotun musamman ta kasar Bangaladash ta yanke hukuncin kisa wa daya daga cikin shugabannin jam'iyyun adawa na kasar, bisa laifukan yaki na shekarar 1971 lokacin yakin kwatar 'yanci daga Pakistan.Motiur Rahman Nizami dan shekaru 71 kana tsohon minista da ke jagorancin jam'iyyar masu ra'ayin kishin Islama an yanke masa hukuncin a wannan Laraba.

Magoyan bayan jam'iyyar da suka harzika sun yi zanga-zanga jim kadan bayan yanke hukuncin. A shekara ta 2010 Firaministar kasar ta Bangaladash Sheikh Hasina ta kafa kotun shari'ar wadanda ake zargin da aikata laifuka a shekarar 1971 kimanin shekaru 43, yayin yakin neman 'yanci daga Pakistan, abin da 'yan adawa ke dauka a matsayin yarfen siyasa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe