1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kisa ya karu a wasu kasashen Afrika

March 27, 2014

Rahotan Amnesty International na 2013 ya nunar da cewar, Najeriya na cikin kasashen Afrika da ake ci gaba da aiwatar da hukuncin kisa.

https://p.dw.com/p/1BXU5
Symbolbild Todesstrafe Amnesty International
Hoto: dapd

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa ta Amnesty International ta bayyana damuwa dangane da karuwar aiwatar da hukuncin kisa da wajen kashi 50 a wasu kasashen Afrika a shekarata 2013, idan aka kwatanta da shekara ta 2012.

Kungiyar ta Amnesty ta nunar da cewar mafi yawancin kasashen nahiyar Afrika an daina wannan danyen hukuncin, yayin da kadan daga ciki suke ci gaba da aiwatar da shi. Kungiyar ta bayyana takaicinta dangane da cewar a yayin da wasu kasashe ke gyaran kundin tsarin mulkinsu don kawar wannan dabi'a ,har yanzu kasashe kamar Najeriya na ci gaba da aiwatar da shi.

China richtet jährlich 8000 Menschen hin - Fehlurteile und Missstände
Hukuncin kisa a kasar ChinaHoto: picture-alliance/dpa

Masani kan hukuncin kisa a kungiyar ta Amnesty Yarn Welsor ya yi karin haske dangane da wannan batu:

"Muna gudun kada hukuncin kisa ya tsananta a kasashe da dama ba ma a Najeriya kawai ba, amma har da sauran kasashen yammacin Afrika,inda wasu sun daina aiwatar da hukuncin, kana wasu kuma suna kokarin dainawa gaba daya".

A cewar Amnesty International dai kasashe uku da suka hadar da Najeriya, Sudan da Somaliya, na wakiltar kashi 90 daga cikin hukuncin kisa 64 da aka aiwatar a shekara ta 2013. A kan hakane Yarn ya yi tsokaci kan irin hukuncin daya kamata a rika yanke wa masu laifi a madadin na kisa:

Ya ce: Idan mutum ya aikata mummunan laifi za'a iya yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari,ko kuma a hada masa da wasu horo domin babu wanda ya wuce a hukuntashi'".

Hinrichtungsraum Gefängnis Abu Ghraid Irak
Igiyar rataye mutaneHoto: picture alliance/dpa

A karon farko cikin shekaru bakawai da suka gabata,Najeriya koma aiwatar da hukuncin kisa, inda a watan Yuni ne aka zartar da hukuincin akan wasu mutane hudu.Akan wannan hali dai ga abunda kwararren na kungiyar Amnesty Yarn....

Ya ce:" Shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ne ya amince da zartar da hukuncin na kisa a kan duk wadda aka yankewa, amma yanzu muna farin ciki kasancewar ministan shari'ar kasar ya tabbatar da cewar, Najeriya zata bi umurnin kotun ECOWAS, na dakatar da aiwatar da hukuncin kisa, kamar yadda kotun ta umurta a farkon wannan shekara ta 2014".

Sai dai rahotan na shekara ta 2013 na kungiyar ta Amnesty, ya yabawa irin cigaba da aka samu a kasashen nahiyar ta Afrika. Inda a cewarta sama da kashi biyu daga cikin uku, wanda ke wakiltar kasashe 37 daga cikin kasashen Afrika 54, sun daina aiwatar da hukuncin kisa a hukumance.

Mawallafiya: Zainab Babbaji Katagun
Edita : Zainab Mohammed Abubakar