1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kissa a Somalia

July 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuGv

Kotu a birnin Mogadiscio na ƙasar Somalia, ta yanke hukunci kisa, ga wasu mutane 2, da aka samu da leffin kissan Osman Ali, mai unguwar Horuwa, wata unguwa da ke birnin na Mogadiscio.

A yau a ka bindige mutanen 2, a bainin jama´a.

Wannan shini hukunci mafi tsanani ,da kotu ta taɓa yankewa a ƙasar Somalia, tun bayan girka gwamnatin riƙwan ƙwarya a shekara ta 2004.

Hare-hare a Somalia ya ƙara tsamari tun shigar dakarun Ethiopia a wannan ƙasa domin tallafawa gwmantin wucin gadi.

Haren bayan bayan ne sun wakana a jiya laraba, wanda su ka rusta da magajin garin Mogadiscio, da kuma mataimakin ministan shari´a.

Kazalika maharan, su abkawa babban opishin yan sanda da ke wannan birni, ba tare da cimma buri ba.