1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kotu akan taƙaddamar zaɓen Najeriya

December 28, 2011

A wani hukunci da zai tasiri ga dimukurɗiyyar Najeriya kotun ƙolin ƙasar da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar adawa ta CPC ta gabatar na cewar an tafka maguɗi a zaɓen shugaban Najeriyar

https://p.dw.com/p/13af1
Gen. Muhammadu Buhari, presidential candidate of the Congress for Progressive Change, attends a campaign rally in Lagos, Nigeria, Wednesday, April 6, 2011. Buhari, a former military ruler of Nigeria, has gained support in his third bid to become president of the oil-rich nation. Buhari ruled Nigeria from 1983 to 1985 after a military coup deposed the elected president. (AP Photo/Sunday Alamba)
Janar Muhammadu BuhariHoto: AP

Bakin ɗaukacin alƙalai guda shida da suka yanke hukunci a wannan shari'a mai tarihi a kotun ƙolin Najeriyar sun amince bisa kan cewa ƙarar da jam'iyyar CPC ta Janar Muhammadu Buhari ta gabatar ta gaza samar da shaidun cewa an saɓa ƙa'idar dokar zaɓe ta 2010 a wajen gudanar da zaɓen tare da nuna cewar ko hakan ya lahanta ɗaukacin zaɓen kansa.

Alaƙalin da ya jagoranci shari'ar a kotun ƙolin Najeriyar Olufunmilayo Adenike ya ce sashi na 36 na tsarin mulkin Najeriyar ya ɗora nauyin ba da shaidar an tafka maguɗi a kan wanda ya kai ƙara kuma gazawar haka ya sanya dole su yi watsi da ƙarar.

Tuni dai jam'iyyar adawa ta CPC ta yi watsi da hukuncin duk dai da sanin cewar kotun ƙolin ce ta ƙarshe da jam'iyyar zata iya ɗaga batun.

A nata ɓangaren a hanzarce jam'iyyar PDP ta yi murana da sakamakon kotun, inda tawagar ministoci suka halaraci zaman kotun.

To sai dai ga lauyan da ya kare shugaban ƙasa Alex Ezion ya ce wannan muhimmin ci gaba ne yadda aka fito da wannan batu mai sarƙaƙiya.

Ya ce kotun ƙoli ta ɗauki lokaci ta fito da wannan matsala ta nauyin tabbatar da an aikata laifi da aka ɗora wa wanda ya kai ƙara, kuma wannan zai taimaka mana a kotun ɗaukaka ƙara da ma sauran kotunan da ake shari'a, ba zaka ce ba a yi zaɓe ba ka tsaya, kotun ƙoli ta ce dole ne in ka ce ba a yi zaɓe ba nauyin kanka yake ka tabbatar da hakan.

Da wannan hukunci shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai miƙe ƙafa sosai wajen gudanar da mulkin ƙasar da kotun ta halatta zaɓensa. To sai dai mulkin Najeriyar na fuskantar ƙalubale mai yawa kama daga rashin tsaro na ja-in-ja da ake yi a game da janye tallafin mai wanda yan Najeriya ke adawa da shi. Lokaci ne dai zai nuna ko shugaban zai samar da sabuwar iskar da ya yiwa 'yan Najeriya alkawari a lokacin yaƙin neman zabensa.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris

Edita: Ahmad Tijani Lawal