1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hulɗar diplomasiyya tsakanin Masar da ƙasashen duniya

Knipp Kersten / MAApril 2, 2015

Shekaru huɗu bayan kawar da Hosni Mubarak daga karagar mulkin Masar, gwamantin ta yi nasarar farfaɗo da dangantaka da sauran ƙasashe.

https://p.dw.com/p/1F29S
Ägypten Reaktion auf Ermordung koptischer Christen durch IS
Abdel Fattah al-Sisi shugaban ƙasar MasarHoto: imago/Xinhua

Fadar mulki ta Alƙahira ta yi amfani da angizon da take da shi a Yankin Gabas ta Tsakiya wajen daidaita dangantakarta da manyan ƙasashen yammacin duniya.

Amirka ta ɗage takunkumi haramta sayar da makamai ga Masar

Gwamnatin Amirka ta ɗage takunkumi sayar da makamai da ta ƙaƙaba wa Masar, tare ma da farfaɗo da dangartakar tsaro da ke tsakanin ƙasashen biyu. Wannan ya na nufin cewar fadar mulki ta White House za ta sake fara sayar wa hukumomin Masar da jiragen yaƙi da suke buƙata. Ko da a lokacin da ya tsokaci a kan wannan mataki a ƙarashen watan Maris, sai da shugaban Amirka Barack Obama ya yi alƙawarin taimaka wa Masar da miliyan 1300 a fannin tsaro.Wannan matakin dai ya bai wa shugabannin ƙasashen biyu damar farfaɗo da dangataka da ta yi tsami tsakaninsu, tun bayan da guguwar neman sauyi ta kaɗa a Masar, tare da yin awon gaba da mulkin Mubarak da kuma Mursi. Da farko dai Amirka ta katse kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninta da Masar kafin daga bisani ta lashe amanta bayan da Abdul fatah al-Sisi ya ɗare kan kujerar mulki.

Kerry mit Al-Sisi in Kairo 22.07.2014
Abdel Fattah al-Sisi tare da sakataran harkokin wajen Amirka John KerryHoto: Reuters

Ƙarfafa hulɗa tsakanin Masar da sauran ƙasahen duniya

Ita dai Masar ta na ci gaba da zama ɗaiɗaiku Ƙasashen Larabawa da ba a samun rikicin da ya zarta hankali a cikinsu. saboda haka ne wasu manyan ƙasashen duniya ke neman damawa da ita wajen gano bakin zaren warware rikici-rikice da suka addabi Libiya da Syriya da kuma Iraƙi. Baya ma dai ga ƙasar Amirka, ita ma Saudiyya ta bi sahu wajen neman haɗin kan Masar don yaƙar 'yan Shi'an Huthis da suka ƙwace mulki a Yemen. Amma kuma Iran da ke mara wa 'yan Huthis baya ta ce ba za ta taɓa ƙyale Saudiyya da Masar da sauransu su yi abin da suka ga dama a Yemen ba, a ta bakin Kanani Moghadam, tsohon komandan rundunar juyin-juya-hali na Iran

Schweiz Weltwirtschaftsforum in Davos
Abdel Fattah al-Sisi tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa/F. Coffrini

"Idan Saudiyya da ƙawayenta ciki har da Masar da Qatar da Kuweit da Bahrain suka ci gaba da kai hare-hare tare da matsa wa Yemen lamba, to lallai Iran za ta tura da mashawarta a fannin tsaro da nufin taimaka wa Yemen, kamar yadda ya faru a Siriya da kuma Iraƙi."

Sai dai kuma Saudiyya na alfahari da samun haɗin kan shugaba al-Sisi na Masar wajen saka ƙafar wando guda da duk wasu abubuwa da ke barazana a gareta. Na farko dai Ƙungiyar 'yan Uwa Musulmi da Saudiyya ke ɗauka tamkar wata barazana ga makomar mulkin gado da ƙasar ke gudanarwa, saboda ta na iya tunzura ɗaukacin Ƙasashen Larabawa ga yin bore. Yanzu haka dai ƙasashen yankin Golf da dama ciki har da Saudiyya sun taimaka wa Masar da kuɗaɗe domin ta gudanar da aiyyukan raya ƙasa. Kana su ƙarfafa hulɗar da suke da ita tsakaninsu a fannin tsaro.