1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Huldar Rasha da Siriya

Usman Shehu UsmanJune 18, 2016

Shugaba Bashar al Assad ya gana da ministan tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu ganawar wace aka yi a birnin Damaskus, an fi maida hankali kan taimakon da Rasha ke baiwa gwamnatin Siriya bisa yakar kungiyoyin 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/1J9Ll
Syrien Russischer Bomber wirft Bombe ab
Hoto: picture-alliance/dpa/Russian Defence Ministry's Press and Information Department/TASSpicture-alliance/dpa/Russian Defence Ministry's Press and Information Department/TASS

Gidan talabijin din gwamnatin Siriya bai yi wani karin haske ba kan ziyar bazata da Sergei Shoigu ya kai Damaskus, sai dai an bayyana cewa ministan tsaron na Rasha ya je Siriya ne bisa umarnin shugaba Vladimir Putin. Don karfafa tsare-tsaren aiki tare tsakanin sojojin Siriya da na Rasha, ta yadda za su ci gaba da fatattakan 'yan ta'adda.

Birnin Aleppo dai yana daga cikin inda hankali ya fi karta a rikicin na Siriya, inda wannan mutumin ke cewa.

"Jiragen yaki sun kai farmaki a anguwar Fardous da safiyar yau. da kuma anguwannin Bstan al Qaser da Bab al Nairab. Da sanyin safiya sai muka ji makamai masu linzami na sauka. Harin ya ritsa da mutane cikin buraguzai, amma dai mun gode wa Allah domin duk mun zakulo su".

A 'yan kwanakinnan dai gwamnatin Siriya na ci gaba da yin galaba kan 'yan tawaye da 'yan ta'adda, wannan kuwa godiya ta tabbata ga tallafin kasar Rasha.