1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fi take hakkin jama'a a Saudiyya da China

January 17, 2019

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch ta fitar da rahotonta na shekarar 2019 a wannan Alhamis, inda musamman batun take hakin dan Adam a kasashen China da Saudiyya ya mamaye.

https://p.dw.com/p/3Birj
Ramallah -  Digital Activism Forum
Hoto: DW/T. Tox

Wenzel Michalski shi ne daraktan kungiyar ta Human Rights Watch a Jamus, da a wannan rana ta Alhamis ya gabatar da rahoton kungiyar na shekarar 2019 mai shafuka kusan 400 da ya jawo hankali kan batutuwan da suka shafi hakin dan Adam. A bana kasar da hankali ya koma kanta kamar yadda Michalski ya nunar a hira da tashar DW ita ce kasar China.

Ya ce: "Babu labari mai dadin ji daga China, babu damar fadin albarkacin baki, ana murkushe kungiyoyin fara hula, wadanda da ma yawansu bai taka kara ya karya a cikin kasar ba. Shugaba Xi Jinping na kara zama dan kama karya. Wani abin damuwar ma shi ne gwamnatin China na yada manufofinta na take hakin dan Adam a kasashen duniya da take ba su taimakon raya kasa."

Tun a 1989 Human Rights Watch ke wallafa rahoto da ke mayar da hankali kan gwamnatocin mulkin kama karya da ke fatali da hakkin al'ummominsu. Baya ga gwamnatin China a bana kungiyar ta kuma soki lamiruin shugaban Amirka Donald Trump musamman dangane da matakan karfi da yake dauka kan 'yan gudun hijira daga yankin Latun Amirka. Ita kasar Saudiyya an tabo ta, saboda kisan dan jaridar nan Jamal Kashoggi da kuma mummunan yakin da take jagoranta a kasar Yemen tun a 2014.

Wenzel Michalski direktan Human Rights Watch a Jamus
Wenzel Michalski direktan Human Rights Watch a JamusHoto: DW

Take hakin dan Adam a wasu kasashen Turai irin su Poland da Hungary da yadda ake samun jam'iyyun masu kyamar baki a nahiyar ya dauki hankalin masu fafatukan kamar yadda daraktan na kungiyar Human Rights Watch a Jamus Wenzel  Michalski ya nunar.

Ya ce: "Take-taken gwamnatoci a kasashe irin su Hungary da Poland da ma a Italiya sun dauki hankalinmu. Ga misali ministan cikin gidan Italiya Salvini ya yi fatali da 'yancin masu neman mafakar siyasa na yi musu adalci wajen duba bukatunsu. A Hungary Firaminista Viktor Orban na kaskantar da tsiraru a kasarsa don samun goyon bayan masu zabe, a Poland an yi kokarin tauye 'yancin shari'a."

Ita ma tarayyar Jamus ta sha suka dangane da makaman yakin da take sayarwa kasar Saudiyya da Human Rights Watch ta ce hanyoyi na sirrin da ake bi na wannan ciniki na da daure kai. Michalski ya ce a kasa mai bin tsarin da doe a ba wa al'ummar damar bayyana ra'ayinsu. Amma ya ce Jamus ta fara farga da irin nauyin da ke kanta a siyasar duniya.

Ya ce: "Muna ganin yadda Jamus ke ba da himma wajen daukar karin nauyi a fagen siyasar duniya. Tana kara fitowa fili tana sukar yadda ake take hakin dan Adam."

Kungiyar ta nuna farin ciki yadda kungiyoyin farar hula ke kara ba da himma, abin da ke kara nuna turjiya ga 'yan mulkin kama karya a duniya.