1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hurucin kungiyoyin kare haƙƙoƙin jama´a a game da mace-macen Guantanamo

Yahouza Sadissou MadobiJune 12, 2006

Ƙungiyoyin kare haƙƙokin bani adama sun yi tur ga gwamnatin Amurika, bayan mace-macen Guantanamo

https://p.dw.com/p/Btzl
Hoto: AP

Idan dai za iya tunawa, a shekaran jiya ne, a ka gano gawwawakin wasu Pirsinoni 3, da tsare da sansanin Gwale gwalen Guantanamo na ƙasar Cuba.

Wannan mutane sun haɗa da 2 na Saudiya, 1 na ƙasar Yamal.

Fadar Gwamnatin Amurika, ta bada rahoton cewar sun kashe kann su ne.

Saidai iyalen mamatan sun nuna shaku da wanan rahoto.

Lauyan mutanen 2, na Saudiya ya ce, ya na da matuƙar wuya wannan mutane su rataya kansu, ta la´akarai da tsatsauran matakan tsaro da ke dakwai ,a wannan gidan yari, inda dare da rana, a na sa ido kan su ,da na´urori masu ɗaukar hoto na zamani.

Ya ce, kawai wannan rashi na nuni ƙarara uƙuba da azaba da Amurikawa ke ganawa Prisinonin Gwantanamo.

Hukumar ƙwatar yanci ta dunia CCR, da ta ƙunshi lauyoyi fiye da 200, masu kariyar prisinonin Gwantamo, sun yi tur da Allah wadai, ga gwamnati Shugaba Bush, da ido rufe, ta girka haramtacen sansanin gwale-gwalen Guantanamo, tun shekara ta 2002, da niyar yaƙi da ta´adanci.

Mafi yawan mutanen da ake tsare da su,a ciki, an yi farautar su daga ƙasar Afghanistan, a shekara ta 2001, a lokacin da Amurika ta buɗe yaƙi da yan taliban.

Daga cikin pirsinoni 460 da ke tsare a halin da ake ciki, 10 kaɗai a ka bayana wa leffin da ake tuhumar su da aikatawa, kuma suma har yanzu, ba a yi masu shari´a ba.

A nata ɓangare hukumar kare haƙƙoƙin bani adama, da dunia Amnisty International, ta sake jaddada kira ga Amurika da ta rufe wannan gidan yari.

Shima kakakin Majalisar Ɗinkin Dunia a game da harakokin ƙuntatawa jama´a, Manfred Nowak, wanda a watan Februaru ya gabatar da rahoto a game da matsanancin halin da pirsinonin Guantanamo ke ciki ya, buƙaci hukumomin Amurika, su rufe wannan gida.

Hukumar ta yi kira ga ƙasashen Turai, da za su gana da shugaba Bush ranar 21 ga watan da mu ke ciki, da su yi anfani da wanan dama, domin matsa masa ƙaimi, ya kulle Gwantanamo.

Komitin ƙasa da ƙasa na Red Cross, ya bayyana tura wata tawaga ta mussaman, domin gudanar da bincike a kan ainahin mussababbin mutuwar mutaten 3.

Wani labari da jaridar New York Time, ta buga ya nunar da cewa, gwammnatin Amurika ta laya mutanen 3, a sahun cikkakun yan ta´ada.

Saidai a ta bakin Arlen Specter, wani ɗan majalisar dattawan Amurika,na jam´iyar Repubilkan, al´amarin da ya wakana a Gwantanamo, ranar assabar ya issa ya zama darasi ga Amurika.

A halin yanzu dai, tunni ƙasar Saudiya Arabia, ta fara bin hanyoyin jiggilar gawawakin yan ƙasar ta 2, da ke cikin wanda su ka mutun.