1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC ta daure Bemba shekaru 18

Suleiman BabayoJune 21, 2016

Kotun duniya da ke hukunta masu laifukan yaki da ke birnin Hague, ta daure shi ne bisa laifukan da dakarunsa na sa-kai suka aiwatar a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1JAim
Niederlande Internationaler Strafgerichtshof Prozess gegen Jean-Pierre Bemba in Den Haag
Hoto: Reuters/P. Dejong

A zaman da alkalai suka yi a kotun na ICC da ke kasar Holland, sun yanke hukuncin daurin shekaru 18 ga Jean-Pierre Bemba tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo, bisa laifukan da dakarunsa na sa-kai suka aiwatar a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Bemba dan shekaru 53 da haihuwa tun cikin watan Maris kotun ta same shi da laifi kan lamarin ta'asa na shekara ta 2002 zuwa 2003 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da suka hada da fyade kuma ya kasance na farko da kotun ta samu da laifi bisa aikin da dakarun da ke karkashin ikonsa suka aikata. Ita dai kotun ta duniya ta kama Bemba da laifui saboda yadda ya gaza tsawatar wa dakarun da ke karkashin ikonsa.