1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Illar Ebola ga tattalin arzikin yammacin Afirka

August 8, 2014

Kamfanonin jiragen sama na Afirka da na ƙasashen waje kamar British Airways da Emirates sun sanar da dakatar da zirga-zirga zuwa ƙasashen da ake da Ebola.

https://p.dw.com/p/1Crce
Ebola Westafrika
Hoto: picture alliance/AP Photo

Ɓullar cutar Ebola dai ya haifar da tsaiko a harkoki na rayuwa a ƙasashen da abin ya fi shafa da ma waɗanda ke ɗaukar matakai na riga kafi. Harkokin kasuwanci, tattali da ayyuka dai na fuskantar raɗaɗin wannan cuta, musamman a cikin ƙasashen Liberia da Saliyo da Gini.

Tsaiko na harkokin kasuwanci a cikin ƙasashen da Ebola ta ɓulla

Caesar Morris wani mai shagon harkar sadarwa da buga waya ne a birnin Monrovia fadar gwamnatin Liberia. Kuma a cewarsa harkokin kasuwanci ba su taɓa tsaya masa cik kamar yanzu ba:

Ebola Westafrika
Hoto: Reuters

"Cutar Ebola ta shafi yanayin rayuwarmu . An tsayar mana da harkokinmu na kasuwanci a yayin da wasu suka samu tsaiko".

A yanzu haka dai mutane ba su da sukunin gudanar da rayuwarsu cikin walwala, tun bayan da gwamnati ta ɗauki tsauraran matakai na kariya. Wannan matakai dai kamar yadda ya shafi wasu masu shaguna na kasuwanci, ya shafi Moris mai shagon shayi a Monrovia.

"Tun bayan ɓullar cutar, kafin mutum ya shiga ƙofar wannan cibiya tamu , sai ya bi ta kan wani ƙyalle da ke shimfuɗe wanda aka jiƙa da wasu sinadarai, kana ya isa wani wurin da aka ajiye ruwa na wanke hannu kafin ya samu shiga".

Kamfanoni sufiri na ƙasashen ƙetare sun dakatar da zirga-zirga a cikin ƙasashen masu Ebola

A watan Maris na wannan shekarar nan ce dai aka tabbatar da mutumin farko da ya kamu da wannan cuta a ƙasar Gini. Jim kaɗan ne kuma cutar ta yaɗu zuwa Liberia da Saliyo da ke maƙwaɓtaka. Akasarin waɗanda ke kamuwa da cutar dai suna mutuwa. Ƙididdigar Hukumar kula da Lafiya ta MDD na nuni da cewar aƙalla mutane 932 suka mutu kawo yanzu. Bayan kamfanin Arik dai suma manyan kamfanonin na ƙetare kamar Emirates da British Airways tun a ranar Talata suka sanar da dakatar da zirga-zirga zuwa ƙasashen da wannan matsala ta shafa kama daga ƙarshen wannan watan.

Ebola Flugzeug Rückkehr spanischer Geistlicher Miguel Pajares
Hoto: picture-alliance/dpa

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdourahamane Hassane