1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta fannin ilimin magungunan gargajiya

April 16, 2014

Samar da fannin koyar da ilimin magungunan gargajiya a jami'o'in Najeriya, da nufin sanya harkokin magungunan na gargajiya su rinka tafiya dai dai da zamani.

https://p.dw.com/p/1BjZ7
Bildergalerie Voodoo in Westafrika
Hoto: DW/K. Gänsler

Ma'aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya ta bayyana cewa dukkanin shiri ya kammala wajen ganin an kai ga fara koyar da darussa kan ilimin magungunan gargajiya a jami'o'in da ke fadin Najeriya, da nufin ganin cewar masu magungunan gargajiyar sun bi sahun tsarin kula da harkokin lafiya na zamani da ke da bukatar gudanar da bincike kan cututtuka kafin bada magani cikin ka'ida.

Gwamnatin ta Najeriya dai ta bayyana hakan ne a wani taron kungiyar masu ruwa da tsaki a harkokin kula da lafiya a kasar. Taron ya kuma tabbatar da cewar kafin a cimma kudirin samar da ingantacciyar lafiya ga jama'a, to dole ne a samu hadin kan masu magungunan gargajiya da ke kasar. To sai dai ma'aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya ta nunar a gurin taron cewar, hadin kai da masu bada magungunan gargajiya shi ne kawai a ilimantar da su hanyar kula da lafiya a zamanance, ta yadda dole a karantar da su ilimin sanin jikin mutum da kimiyyar magunguna da cututtuka da sauransu.

Manufar da ake son cimmawa

Zusammenstellung verschiedener Gewürze
Sauyoyi da wasu ganyaye na taka rawa wajen harhada magungunan gargajiyaHoto: Fotolia/photocrew

Dr Abubakar Sokoto Muhammad na daya daga wadanda suka gabatar da bayani a gurin taron, ya bayyana fahimtarsa ga tsarin da ake son cimmawa.

"Tsarin kiwon lafiyarmu a Najeriya na wanda Turawa suka shigo da shi ne, amma saboda tsadarsa mafi yawancin talakawanmu ba su da kudin biyan yadda za su samun wannan kiwon lafiya, shi ya sa suke zuwa wurin na gargajiya. Sauran kasashen duniya ma suna aiki da na gargajiyar, amma ana son shi ma ya bi kyakkyawan tsari na zamani, musamman wajen bada magani da kuma binciken lafiya kafin a bada maganin."

Wani Mallam Adamu Wanzam kan bada magungunan gargajiya, cewa ya yi "jama'a na raja'a kan magungunan na gargajiya da yadda wani magani daya tilo ke maganin cututtuka daban-daban".

Ci gaba a kokarin inganta kiwon lafiya

Traditionelle Chinesische Medizin in Ottobeuren
Akwai cibiyoyin kiwon lafiya ta hanyar gargajiya da yawa a ChinaHoto: picture-alliance/dpa

Dr Nura Sani, malamin jami'a ne a Najeriya da ke koyar da fannin ilimin sinadarai wato Biochemistry, ya bayyana yadda za'a samu nasarar abin da ake son cimmawa da kuma irin ci gaban da ake samu a kasar.

"Idan aka yi kyakkyawar fadakarwa, jama'a za su yarda su bada hadin kai. Misali a Kano an fara wannan shiri na inganta harkokin magungunan gargajiya. Sannan a duk lokacin da za a yi taro kan magungunan gargajiya a Jami'ar Ahmadu Bello ana gayyato sarakunan masu magungunan gargajiya domin su zo su baje kolin magungunansu. Ana samun tattaunawa da fahimtar juna."

Yanzu dai ta tabbata cewar akwai tsananin bukatar da jami'an kula da harkokin lafiya din a gargajiyance da su rungumi tsarin na zamani dan a samu tsafta a harkokin kula da lafiya a kasar.

Babban dai kalubale shi ne yadda za a cimma yarjejeniyar samun sirrin magungunan da masu magungunan na gargajiya ke tattare da shi.

Mawallafi: Muhammad Bello
Edita: Mohammad Nasiru Awal