1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki ta yaba salon yaki da ta'addanci na Trump

Salissou Boukari
March 21, 2017

Yayin wata ziyara da ya kai a Amirka, Firaministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya ce gwamnatin Shugaba Donald Trump ta fi ba da karfi kan yaki da ta'addanci fiye da gwamnatin baya ta Barack Obama.

https://p.dw.com/p/2ZbSR
Irak Premierminister Haider Al-Abadi  in Kirkuk
Firaministan kasar Iraki Haider Al-Abadi

Firaministan na Irki ya yi wannan kalami ne bayan ganawarsa da shugaban na Amirka a fadarsa ta White House ko kuma Maison Blanche, inda Shugaba Trump ya jaddada aniyarsa ta ganin bayan kungiyar IS yana mai cewa:

"Babban burinmu shi ne na kawo karshen kungiyar IS, kuma muna kan haka, za mu ga bayansu, domin Janar Mattis da tawagarsa suna aiki mai kyau.  Abubuwa da dama sun sauya kan yadda a makwanni biyar zuwa shidan da suka gabata, don haka muna tare da ku, kuma mun gode da wannan ziyara ta Firaminista."

Bayan ganawarsa da Shugaba Trump, Firaministan na Iraki ya sanar cewa taimakon da Amirka ke bayarwa wajen kwato birnin Mosul na habaka cikin gaggawa a karkashin mulkin Shugaba Trump.